Ku Fada Wa Masu Neman Canji a Najeriya Su Rufe Bakunansu, Tinubu Ga Jirgin Kamfen Mata

Ku Fada Wa Masu Neman Canji a Najeriya Su Rufe Bakunansu, Tinubu Ga Jirgin Kamfen Mata

  • Ɗan takarar shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya nemi matan APC su gaya wa masu neman canjin gwamnati su yi wa mutane shiru
  • Tsohon gwamnan jihar Legas ɗin yace jam'iyyar APC ta hau gadon mulki lokacin da ƙasar nan ke cikin yanayi mai muni
  • A ranar Litinin, 10 ga watan Oktoba, 2022 jam'iyyar APC ta kaddamar da tawagar mata da zata tallata Tinubu/Shettima

Abuja - Mai neman zama shugaban ƙasa a inuwar APC, Bola Tinubu, ya nemi matan jam'iyyar su gaya wa yan Najeriya dake son canjin gwamnati, "Su rufe bakinsu."

Jaridar The Cable ta tattaro cewa Tinubu ya faɗi haka ne a wurin kaddamar da tawagar kamfen APC ta mata ranar Litinin a Abuja.

Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Ku Fada Wa Masu Neman Canji a Najeriya Su Rufe Bakunansu, Tinubu Ga Jirgin Kamfen Mata Hoto: thecableng
Asali: UGC

Tinubu yace mutanen da ke neman canji sun manta halin da kasar nan ke ciki kafin shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya karɓi mulki.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Fitaccen Dan Siyasa Kuma Na Kusa da Dan Takarar Shugaban Kasa Ya Rasu

Tsohon gwamnan jihar Legas ɗin ya ƙara da cewa zai kawo ƙarshen ta'addancin 'yan fashin daji da zaran ya zama shugaban ƙasa a zaɓen 2023.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Idan sun ce suna bukatar canza gwamnati ku faɗa musu, zamu so a baje komai a fai-fai, amma su gimtse bakunansu," inji Tinubu.

"Gare ku mutanen da suka hallara anan musamman mata, bari na gaya muku, fata, alƙawari tsaro sun dawo, fashin daji ya ƙare sannan kuma rashin tabbas ba ya daga cikin ƙamus dinmu."
"A shekara Takwas da suka wuce, jam'iyyar data gaji ƙasa cikin matsala da rashin madafa, muka zo da zancen canjin gwamnati kuma Allah ya canza."
"Buhari ya ɗare madafun iko, lokacin ana hako gangar mai mafi karanci, ganga 400,000 a kowace rana, farashi ya faɗi warwas, amma duk da haka ya cije ya jajirce har ya tsamo jihohi 36, waɗanda basu iya biyan albashi."

Kara karanta wannan

Tinubu, Atiku Ko Kwankwaso? An Bayyana Dan Takarar Da Ya Shirya Ceto Najeriya Idan Ya Gaji Buhari a 2023

- Bola Tinubu.

A wani labarin kuma Jam'iyyar ADC Ya Kori Tsohuwar Shugabar Majalisar Dokoki da Wasu Jiga-Jigai a Jihar Oyo

Jam'iyyar African Democratic Congress, (ADC) ta kori mace ta farko da ta rike kujerar kakakin majalisar dokokin jihar Oyo , Monsurat Sunmonu.

ADC ta ɗauki matakin korar Monsurat tare da wasu jiga-jigan jam'iyyar.saboda sun goyi bayan tazarcen Seyi Makinde, gwamnan jihar Osun na jam'iyyar PDP.

Asali: Legit.ng

Online view pixel