Gwamna Wike da Wasu Kusoshi da Suka Ki Halartar Taron Fara Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa Na PDP

Gwamna Wike da Wasu Kusoshi da Suka Ki Halartar Taron Fara Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa Na PDP

  • Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike ya kauracewa taron kaddamar da kamfen din takarar shugaban kasa na PDP da aka yi a jihar Akwa-Ibom
  • Gwamnan jihar Abia, Okezie Ikpeazu, takwaransa na jihar Oyo, Seyi Makinde da na jihar Enugu, Ifeanyi Ugwuanyi duk basu halarci taron ba
  • Wike da mukarrabansa suna adawa da kasancewar yan arewa a matsayin dan takarar shugaban kasa da shugaban jam'iyyar na kasa a lokaci guda

Akwa-Ibom - Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, bai halarci kaddamar da kamfen din takarar shugaban kasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ba.

A ranar Litinin, 10 ga watan Oktoba ne aka kaddamar da kamfen din na babbar jam'iyyar adawa a jihar Akwa-Ibom.

Mukarraban Wike da suka hada da gwamnan jihar Abia, Okezie Ikpeazu, takwaransa na jihar Oyo, Seyi Makinde da na jihar Enugu, Ifeanyi Ugwuanyi duk sun kauracewa taron, Channels tv ta rahoto.

Kara karanta wannan

2023: Ana Shirin Bude Kamfe Yau, Atiku Ya Dauki Matakin Karshe Kan Rikicinsa da Gwamna Wike

Nyesom Wike
Gwamna Wike da Wasu Kusoshi da Suka Ki Halartar Taron Fara Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa Na PDP Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Rashin zuwansu wajen taron ba zai rasa nasaba da dagewar da tsagin Wike yayi na cewa dole shugaban PDP na kasa, Iyorchia Ayu, ya yi murabus.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Tsagin Wike sun yi korafin cewa babu yadda za a yi ace yan arewa ne ke rike da mukaman dan takarar shugaban kasa na PDP da kuma na shugaban jam’iyyar na kasa.

Sai dai kuma, Ayu ya sha alwashin ci gaba da zama a matsayin shugaban jam’iyyar na kasa kuma Atiku ya nuna cewa ba zai tilasta shi barin kujerarsa ba.

A watan Satumba, bangaren Wike ya sanar da janyewarsa daga kwamitin kamfen din Atiku.

Duk da rashin hallaran tsagin Wike, PDP ta kaddamar da kamfen dinta a garin Uyo, babban birnin jihar Akwa-Ibom, jaridar Independent ta rahoto.

Kara karanta wannan

A Karon Farko, Wani Gwamnan Arewa Ya Bi Sahun Su Wike, Ya Nemi Shugaban PDP Na Kasa Ya Yi Murabus

Wadanda suka hallara sun hada da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Atiku Abubakar da abokin takararsa kuma gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa da gwamnan jihar Akwa Ibom, Udom Emmanuel.

Sai gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, takwaransa na Adamawa, Ahmadu Fintiri, tsohon dan majalisa mai wakiltan Kogi ta yamma, Dino Melaye da sauransu.

Rikicin PDP: Atiku Ya Kama Harkokin Gabansa Ba Tare da Wike Ba, Majiyar PCC

A gefe guda, mun ji cewa a yau Litinin 10 ga watan Oktoba, 2022, babbar jam'iyyar hamayya PDP zata buɗe yaƙin neman zaben shugaban ƙasa a Uyo, babban birnin jihar Akwa Ibom.

Jaridar Vanguard ta gano cewa da yuwuwar dan takarar shugaban kasa a inuwar PDP, Atiku Abubakar, ya yanke hukuncin fuskantar abinda ke gabansa da Wike ko babu shi.

Wasu bayanai daga wani na ƙusa da Atiku sun nuna cewa mafi yawan mambobin jam'iyya sun yi watsi da kiraye-kirayen da gwamna Wike na Ribas da yan tawagar ke yi na shugaban PDP, Iyorchia Ayu, ya yi murabus.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: "Ni Ba Waliyyi Bane, Ina Da Nakasu Da Dama", Ayu Ya Yi Martani Kan Zargin Rashawa Da Wike Ya Masa

Asali: Legit.ng

Online view pixel