Akwai Adalci a PDP Sabanin APC: Gwamna Tambuwal Ya Bayyana Bambancin Manyan Jam’iyyun Siyasar Kasar 2

Akwai Adalci a PDP Sabanin APC: Gwamna Tambuwal Ya Bayyana Bambancin Manyan Jam’iyyun Siyasar Kasar 2

  • Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal, ya bayyana cewa jam’iyyar PDP ta nuna adalci wajen tsayar da yan takararta na shugaban kasa
  • Tambuwal wanda shine shugaban kwamitin kamfen din takarar Atiku Abubakar yace PDP ta fi APC sau dubu
  • Gwamnan ya yi ikirarin cewa tikitin Musulmi da Musulmi da APC tayi bai nuna dabi’ar tarayya da ke kundin tsarin mulkin Najeriya ba

Akwa Ibom - Darakta janar na kungiyar yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Aminu Tambuwal, ya ce jam’iyyarsa ta fi jam’iyyar All Progressives Congress (APC) sau dubu.

Jaridar Punch ta rahoto cewa Tambuwal, wanda shine gwamnan jihar Sokoto ya yi bayanin dalilin da yasa PDP ce jam’iyyar da tafi dacewa da zama zabin yan Najeriya a babban zaben 2023 mai zuwa.

Kara karanta wannan

Tashin hankali a PDP yayin da shugabannin magoya baya suka sauya sheka zuwa APC a Sokoto

Tambuwal
Akwai Adalci a PDP Sabanin APC: Gwamna Tambuwal Ya Bayyana Bambancin Manyan Jam’iyyun Siyasar Kasar 2 Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Gwamnan ya bayyana cewa yayin da PDP ta nuna adalci a tikitinta na takarar shugaban kasa, sam tikitin APC bai nuna dabi’ar tarayya ta Najeriya ba.

Tambuwal ya bayyana cewa APC ta haifar da sabani a kasar, yana mai cewa PDP za ta yi aiki don tabbatar da ganin cewa irin haka bai sake faruwa ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gwamnan na jihar Sokoto ya bayyana hakan ne a wajen kaddamar da kamfen din jam’iyyar a ranar Litinin, 10 ga watan Oktoba, a Uyo, babban birnin jihar Akwa Ibom.

Sai dai kuma, ya bayyana cewa PDP tana da tikitin Atiku/Okowa wanda ya tabo kowani bangare na Najeriya.

Punch ta nakalto Tambuwal yana cewa:

“Jam’iyyarmu na son ceto Najeriya da kuma dawo da martabarta ne kuma na yarda yan takarar sauran jam’iyyar ba wai kawai suna adawa da tarayya bane illa suna adawa da kundin tsarin mulkin Najeriya saboda bai nuna halin tarayya na Najeriya ba.

Kara karanta wannan

Su suka bata Najeriya: Tinubu ya caccaki Atiku, ya ce PDP ba za ta lashe zaben 2023 ba

“Muna da tikiti adalci, tikitin Atiku/Okowa ya nuna jam’I da karfin Najeriya kuma ya mutunta halinmu a matsayin kasa kuma jam’iyyarmu na gabatar da wadannan manyan yan Najeriya da ke da karfi da halin nagarta don ciyar da kasar gaba.”

Gwamna Wike da Wasu Kusoshi da Suka Ki Halartar Taron Fara Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa Na PDP

A wani labarin, gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, bai halarci kaddamar da kamfen din takarar shugaban kasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ba.

A ranar Litinin, 10 ga watan Oktoba ne aka kaddamar da kamfen din na babbar jam'iyyar adawa a jihar Akwa-Ibom.

Mukarraban Wike da suka hada da gwamnan jihar Abia, Okezie Ikpeazu, takwaransa na jihar Oyo, Seyi Makinde da na jihar Enugu, Ifeanyi Ugwuanyi duk sun kauracewa taron, Channels tv ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel