Shugabannin Kungiyar Magoya Bayan PDP ta Sokoto Sun Koma APC

Shugabannin Kungiyar Magoya Bayan PDP ta Sokoto Sun Koma APC

  • Shugabannin kungiyar goyon bayan dan takarar gwamnan PDP sun saki layin jam'iyyar sun koma jam'iyyar APC
  • Sanata Aliyu Wammako ne ya karbi sabbin mambobin tare da yi musu alkawarin za a dama dasu
  • 'Yan siyasa a Najeriya na ci gaba da duba rumfa mai sanyi-sanyi domin tunkarar zaben 2023 mai zuwa

Jihar Sokoto - Shugabannin kungiyar goyon bayan jam'iyyar PDP mai suna Ubandoma/Sagir Network a jihar Sokoto tare da daruruwan mambobinsu sun sauya sheka zuwa jam'iyyar APC.

Wannan batu na sauya sheka na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hadimin Sanata Aliyu Wammako, kan harkokin yada labarai Malam Bashar Abubakar ya fitar a jihar ta Sokoto.

Aliyu Wammako ne sanata mai wakiltar mazabar Sokoto ta Arewa a majalisar dattawan Najeriya.

Kara karanta wannan

Akwai Adalci a PDP Sabanin APC: Gwamna Tambuwal Ya Bayyana Bambancin Manyan Jam’iyyun Siyasar Kasar 2

APC ta samu karuwa, mambobin PDP sun saki lema
Shugabannin Kungiyar Magoya Bayan PDP ta Sokoto Sun Koma APC | Hoto: gazettengr.com
Asali: UGC

A cewar Abubakar, kungiyar na kunshe ne da magoya bayan dan takarar gwamnan PDP, Malam Sa'idu Ubandoma da abokin takararsa, Alhaji Sagir Bafarawa, The Nation ta ruwaito.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya ambato shugaban jam'iyyar APC na jihar Sokoto, Alhaji Isa Sadiq Achida da ya karbi sabbin mambobin a madadin Wammako na ba su tabbacin aminci da kaunar juna tunda suka shigo APC.

Alhaji Ahmad Aliyu, dan takara gwamna a jam'iyyar APC a Sokoto ya marabci sabbin mambobin, kana ya yi musu alkawarin damawa dasu dumu-dumu a mulkinsa idan ya gaji Aminu Tambuwal.

Yadda dan takarar gwamna ya tarbe su

Jaridar People Gazette ta naqalto dan takarar gwamnan ta bakin wakilinsa yana cewa:

"Ba za ku yi dana-sanin shigowa APC ba domin jam'iyyar a shirye take ta yiwa dukkan mambobinta adalci.

Kara karanta wannan

Su suka bata Najeriya: Tinubu ya caccaki Atiku, ya ce PDP ba za ta lashe zaben 2023 ba

"Bugu da kari, za ku iya tunawa a lokacin mulkin Wammako a Sokoto, karfafa matasa na daya daga cikin abubuwan da ya ba muhimmanci saboda an ba matasa da dama aikin yi.
"Saboda haka, idan APC ta samu damar mulkin Sokoto a 2023, za mu farfado da ayyukan da gwamnatin PDP ta wofantar domin habaka ci gaban al'umma."

Alhaji Ahmad Labaran, shugaban kungiyar magoya bayan ya tabbarwa dandazon wadanda suka tarbe shi cewa, zai yi aiki wajen ganin APC ta yi nasara a zabe mai zuwa na 2023.

Najeriya Ta Zabi Canji a 2015, Amma Ta Kare da Talauci da Rashin Tsaro

A wani labarin, dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya bayyana cewa, zai kawo karshen talauci da rashin tsaro a Najeriya idan aka zabe shi a 2023.

Tsohon mataimakin shugaban kasan ya bayyana hakan ne a ranar Litinin 10 ga watan Oktoba yayin kaddamar da kamfen dinsa a birnin Uyo na jihar Akwa Ibom, rahoton TheCable.

Kara karanta wannan

An Kori Sanatan Adamawa da ya ki yarda Ya yi wa Tinubu Kamfe Daga Jam’iyyar APC

Atiku, wanda ya saki APC a 2017 ya ce a lokacin da PDP ke mulki, ta dago Najeriya daga zuwa sama kuma ta kai kasar matsayin mafi kyawun tattalin arziki a nahiyar Afrika.

Asali: Legit.ng

Online view pixel