‘Yan Siyasar ’Ci Mu Ci’ Ba Za Su Sake Mulki Ba a Najeriya, Tinubu Ya Caccaki Atiku

‘Yan Siyasar ’Ci Mu Ci’ Ba Za Su Sake Mulki Ba a Najeriya, Tinubu Ya Caccaki Atiku

  • Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC, Bola Ahmad Tinubu ya zargi PDP da kawo koma baya a kasar nan
  • Ya kuma bayyana cewa, bai kamat jam'iyyar ta sake kusantar kujerar mulkin Najeriya ba har abada
  • Jam'iyyun siyasa a Najeriya sun fara kamfen, an fara luguden kalaman nuna adawa da juna a tsakanin 'yan takara

FCT, Abuja - Asiwaju Bola Ahmad Tinubu, dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC ya siffanta jam'iyyar adawa ta PDP da taron gara a yau Litinin 10 ga watan Oktoba.

Tinubu ya bayyana hakan ne a yayin kaddamar da majalisar gangamin kamfen dinsa na mata a fadar shugaban kasa dake Villa a Abuja, Daily Trust ta ruwaito.

Tinubu ya caccaki Atiku
‘Yan Siyasar ’Ci Mu Ci’ Ba Za Su Sake Mulki Ba a Najeriya, Tinubu Ya Caccaki Atiku | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Tsohon gwamnan na jihar Legas ya bayyana kwarin gwiwarsa cewa, jam'iyyar adawa ta PDP ba za ta lashe zaben 2023 mai zuwa ba.

Shekaru 16 amma a banza, Tinubu ya caccaki PDP

Hakazalika, ya zargi PDP da bata shekaru 16 ba tare da kawo wani sauyi ba a kasar nan, inda yace jam'iyyar bata fahimci abin da kasar ke bukata ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya buga misali da cewa, amfani da wutar lantarki dole ne, don haka da a baya PDP ta dukufa a gyara fannin wuta da ba a samu matsalar tattalin arziki a kasar ba.

Daga nan ne Tinubu yace bai kamata PDP ta sake kusantar kujerar mulkin Najeriya ba har abada, rahoton TheCable.

Hakazalika, ya kuma bayyana cewa, 'yan PDP 'yan rashawa ne kuma kowa ya sani.

A bangare guda, ya ba gwamnatin APC ta Buhari uzurin cewa, a shekaru takwas da ta shafe na mulki ta dukufa ne wajen kawo mafita ga jagwalgwalen da jam'iyyar PDP ta bari a tsawon shekaru.

Daga karshe ya yabawa gwamnatin Buhari bisa jajircewa wajen tabbatar da kasar bata samu matsalar biyan albashi ba.

APC Ta Kaddamar da Tawagar Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa Na Mata

A wani labarin, an kaddamar da sashen mata na tawagar kamfen din Tinubu na jam'iyyar APC gabanin zaben 2023 mai zuwa nan kusa.

A halin yanzu ne ake gudanar da kaddamarwar a Banquet Hall dake fadar shugaban kasa a Abuja, uma manyan jiga-jigan APC ne suka samu halarta, ciki har da shugaba Buhari.

Shugaban ma'aikatan shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari ma ya samu halarta, inji rahoton jaridar The Nation.

Asali: Legit.ng

Online view pixel