Rikicin PDP: "Ni Ba Waliyyi Bane, Ina Da Nakasu Da Dama", Ayu Ya Yi Martani Kan Zargin Rashawa Da Wike Ya Masa

Rikicin PDP: "Ni Ba Waliyyi Bane, Ina Da Nakasu Da Dama", Ayu Ya Yi Martani Kan Zargin Rashawa Da Wike Ya Masa

  • A baya, Gwamna Nyesome Wike na jihar Rivers da wasu wasu masu ruwa da tsaki sun zargi shugaban PDP na kasa da almubazaranci da kudi
  • A martaninsa, Iyorchia Ayu ya jajirce cewa kawo yanzu komai a fili ake yinsa a jagoranci da ya ke yi
  • Ayu ya kara da cewa ya rike mukamai a masu muhimmanci a baya a siyasa kuma shi ba waliyyi bane amma tabbas sata baya cikin nakasun da ya ke shi

FCT, Abuja - Iyorchia Ayu, shugaban jam'iyyar PDP na kasa ya dage cewa shi babu ƙumbiya-ƙumbiya da rashin gaskiya a shugabancinsa, The Cable ta rahoto.

Shugaban na PDP ya bayyana hakan ne lokacin da wata kungiya ta tsaffin jami'an jam'iyyar suka kai masa ziyara a Abuja, ranar Juma'a, 7 ga watan Oktoba.

Kara karanta wannan

Ni Ba Ɓarawo Bane: Shugaban PDP ya magantu kan zargin badaƙalar kuɗi

Ayu da Wike
Rikicin PDP: "Ni Ba Waliyyi Bane, Ina Da Nakasu Da Dama", Ayu Ya Yi Martani Kan Zargin Rashawa Da Wike Ya Masa. Hoto: Governors In Action.
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mashawarcin Ayu a bangaren watsa labarai, Simon Imobo-Tswam, ya tabbatar da hakan a ranar Juma'a, cikin wata sanarwa da ya fitar.

Ayu ya ya martani ga Wike da wasu

An yi wa Ayu da kwamitin gudanarwa da ya ke jagoranci wato NWC zargin almubazaranci da kudi, da cewa ba a bayyana ainihin yadda aka kashe kudin siyan fom da aka samu ba.

Nyesom Wike, gwamnan Jihar Rivers, wanda ke cikin wadanda ke neman ganin an cire Ayu, ya zarge shi da karbar Naira biliyan 1 daga hannun wani mai neman zama shugaban ƙasa, yayin da ya ke ikirarin cewa shugaban jam'iyyar na kasa 'gwani ne wurin tafka rashawa'.

Da ya ke magana a ranar Juma'a, Ayu ya ce duk da cewa yana da 'nakasu da dama', sata baya daya daga cikinsu.

Kara karanta wannan

Tinubu ne zai ceto Najeriya: Jigon APC ya ce daga sama Allah ya zabi Tinubu ya gaji Buhari

An ambato yana cewa:

"Ba a kafa PDP don ta zama jam'iyyar hamayya ba. Mun kafa jam'iyyar ne don ta rike mulki da kawo cigaban ƙasa. Kuma aikin da ke gaba na shine dawo da jam'iyyar kan mulki. Ba zan dawamma matsayin ciyaman ba. Yanzu abin da ke gaba ne shine ganin mulki ya dawo hannun jam'iyyar. Ba sata na zo yi ba. Ana iya ganin aikin gwamnati da na yi."

Sata bata ɗaya cikin nakasu da na ke da shi, in ji Ayu

Ya kara da cewa:

"Na rike shugaban majalisar tarayya. Na yi minista sau da dama. A matsayi na na ɗan adam, ina da nakasu, amma sata baya daga cikinsu. Ina lura da abin da tarihi zai ce a kai na, NWC da na ke jagoranci na aiki ne kan gaskiya ta yadda kowa zai iya gani."

Asali: Legit.ng

Online view pixel