Atiku, Ayu, Okowa da Gwamnonin PDP Sun Taru a Bauchi, Za Su Tattauna

Atiku, Ayu, Okowa da Gwamnonin PDP Sun Taru a Bauchi, Za Su Tattauna

 • Jiga-jigan jam'iyyar PDP sun taru a jihar Bahcui domin karbar wasu tarin mambobin da suka sauya sheka zuwa jam'iyyar
 • Hukumar zabe ta amince jam'iyyun siyasa su fara tarukan gangamin kamfen gabanin zaben 2023 mai zuwa
 • Mata a jihar Kudu maso Gabas sun taru domin nuna goyon bayansu ga dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC

Jihar Bauchi - Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya gana da gwamnonin PDP a Arewa maso Gabas da sauran jiga-jigan siyasar yankin.

Wannan ganawa na zuwa daidai lokacin da Atiku ke ci gaba da samun ciwon kai daga gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike kan wasu bukatun da ya gabatar ciki har da na sauke shugaban PDP na kasa.

Atiku da mukarrabansa sun dura jihar Bauchi wani taro
Atiku, Ayu, Okowa da Gwamnonin PDP Sun Taru a Bauchi, Za Su Tattauna | Hoto@ @atiku
Asali: Twitter

Wadanda suka halarci ganawar da aka yi a yau Laraba 5 ga watan Oktoba sun hada da:

Kara karanta wannan

Na Hannun Daman Dankwanbo da Wasu Jiga-Jigan PDP 4 Sun Sauya Sheka Zuwa APC a Gombe

 1. Gwamnan Bauchi, Bala Muhammad
 2. Gwamnan Adamawa, Ahmadu Fintiri
 3. Tsohon shugaban majalisa, Bukola Saraki
 4. Gwamnan Sokot, Aminu Tambuwal
 5. Tsohon gwamnan Jigawa, Sule Lamido
 6. Tsohon gwamnan Neja, Babangida Aliyu
 7. Abokin takarar Atiku, gwamna Ifeanyi Okowa
 8. Shugaban PDP na kasa, Iyorchia Ayu
 9. Sanata Dino Melaye, kakakin kamfen din Atiku
 10. Gwamnan Taraba Darius Dickson Ishaku
 11. Dan takarar gwamnan PDP a Gombe, Dr. Mohammed Jibrin
 12. Dan takarar gwamnan PDP a Taraba Agbu Kefas;
 13. Dan takarar gwamnan PDP a Yobe Shariff Abdullahi
 14. Muhammad Ali Jajari, dan takarar gwamna a Borno

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Jaridar The Nation ruwaito cewa, jiga-jigan na PDP za su karbi sabbin mambobin da suka dawo PDP ne kimanin 25,000 a filin wasa na Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi.

Mata Sun Fito Kwansu da Kwarkwata Domin Nuna Goyon Bayan Tinubu a Jihar Imo

Kara karanta wannan

Gwamnan Jihar Bauchi Ya Bayyana Wanda Zai Lashe Zaben Shugaban Kasa a 2023

A wani labarin, dandazon mata da dama daga yankin su Peter Obi sun yi tururuwar nuna goyon bayansu ga dan takarar shugaban kasan jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu.

A gangamin da jaridar TheCable tace matan sun yi a jihar Imo ta Kudu maso Gabas, matan sun mamaye Hero Square dake Owerri kana suka gangara har zuwa cibiyar manyan taruka ta IICC duk dai a birnin.

Da yake magana yayin da ya karbi dandazon matan, gwamna Hope Uzodinma na jihar ya bayyana jin dadinsa da irin kaunar da suke nunawa dan takarar na APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel