Peter Obi Ya Bayyana Abin da Suka Tattauna a Kai da Ya Hadu da Sanusi II a Kasar Waje

Peter Obi Ya Bayyana Abin da Suka Tattauna a Kai da Ya Hadu da Sanusi II a Kasar Waje

  • Mai martaba Muhammadu Sanusi II ya karbi bakuncin Peter Obi a gidansa da ke kasar Birtaniya
  • ‘Dan takaran shugabancin Najeriyan na 2023 yana kasar Ingila yanzu haka, yana zama da mutane
  • Peter Obi ya bayyana cewa a zamansa Sanusi II, sun tabo batun cigaban kasa da tattalin arziki

England - Sanusi Lamido Sanusi wanda yanzu ya zama Muhammadu Sanusi II ya hadu da ‘dan takaran LP a zaben shugaban kasa watau Peter Obi.

Mista Peter Obi ya yi amfani da shafinsa na Twitter a yammacin yau Asabar, ya sanar da Duniya cewa ya yi zama na musamman da Basaraken.

Obi mai neman shugabancin Najeriya ya daura hotunan zaman na su ne da kimanin karfe 3:00 na yau, ya na kiran Muhammadu Sanusi II da abokinsa.

Kara karanta wannan

Fastoci Da Rabaran-Rabaran Fiye Da 30 Sun Halarci Maulidin Annabi Tare Da Musulmi A Kaduna, Hotunansu Ya Kayatar

Jaridar Osun Defender wanda ta rahoto labarin tace abubuwan da wadannan mutum biyu suka tattauna a zaman da aka yi a Ingila sun shafi Najeriya.

Daga ciki sun tattauna kan harkokin ilmi, kula da al’umma da kuma tattalin arziki wanda Sanusi kwararren masanin tattalin arziki ne da ake ji da shi.

A gajeren jawabin da ya fitar a shafin na sa, Obi yace ya ji dadin haduwar da ya yi da Khalifa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Peter Obi da Sanusi
Peter Obi da Sanusi II a Kasar Waje Hoto: @PeterObi / @Adam_L_Sanusi
Asali: Twitter

Peter Obi ya kira Sanusi II da 'danuwa

“Na hadu da abokina kuma ‘danuwa, Mai martaba Sanusi Lamido Sanusi. Mun bata lokaci tare muna tattauna abubuwan da suka shafi kasa…
…Gyaran al’umma da bambamce-bambamcenmu, ilmi, kula da al’umma, da tattalin arziki, da yanayin amfani da hada abubuwan bukata.
Tattaunawa tayi amfani. Ina matukar godiya gare shi da kyakkyawan tarba da hangen nesa.”

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: "Ni Ba Waliyyi Bane, Ina Da Nakasu Da Dama", Ayu Ya Yi Martani Kan Zargin Rashawa Da Wike Ya Masa

- Peter Obi

Saboda matasa muke yi - PGO

Kafin nan, Ashraf Sanusi Lamido ya wallafa hotunsa tare da mahaifinsa da kuma tsohon gwamnan na Anambra mai burin karbar mulkin Najeriya.

Ashraf Lamido a Twitter yake cewa Peter Obi ya fada masa saboda irinsu watau matasa, yake fafutukar darewa kujerar shugaban kasa a inuwar LP.

“Abin da muke yi, saboda ku ne.” - Peter Gregory Obi.

Tikitin APC ya jawo sabani

Kwanakin baya Elisha Ishiyahu Abbo ya fito yana cewa ba zai goyi bayan ‘dan takaransu na APC, Bola Tinubu a zaben Shugaban kasan 2023 ba.

A yau aka ji labari APC ta kori Sanata Elisha Ishiyahu Abbo wanda yanzu haka Sanatan Arewacin Adamawa ne kuma jigo a jam’iyya mai mulki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel