Fastoci Da Rabaran Fiye Da 30 Sun Halarci Maulidin Annabi Tare Da Musulmi A Kaduna, Hotunansu Ya Kayatar

Fastoci Da Rabaran Fiye Da 30 Sun Halarci Maulidin Annabi Tare Da Musulmi A Kaduna, Hotunansu Ya Kayatar

  • Fasto Yohanna Buru na cocin Christ Evangelical and Life Intervention Ministry Kaduna ya jagoranci fastoci da rabaran-rabaran zuwa wurin bikin Maulidi a Kaduna
  • Fasto Buru, ya ce sun halarci Maulidin ne domin inganta hadin kai, zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin Musulmi da yan uwansu Kirista
  • Buru ya nuna damuwarsa matuka kan halin rashin tsaro a kasar musamman arewa inda ya bukaci mabiya addinan biyu su dage da addu'oin zaman lafiya

Jihar Kaduna - Fastoci daga coci sun tana musuli murnar Maulidi (zagayowar ranar haihuwar Annabi Muhammad, SAW) a filin motsa jiki na Ahmadu Bello da ke Kaduna a ranar Asabar, Nigerian Tribune ta rahoto.

Taron Maulidi
Fastoci Sun Yi Bikin Maulidin Annabi SAW Tare Da Musulmi A Kaduna, Hotunansu Ya Kayatar. Hoto: Nigerian Tribune.
Asali: Facebook

Mun taho don karfafa zumunci ne da hadin kan kasa - Buru

Da ya ke magana a wurin taron gaban dubban musulmi, shuaghan cocin Christ Evangelical and Life Intervention Ministry, Kaduna, Fasto Yohanna Buru, ya ce Maulidi dama ce mai muhimmanci da Kirista za su samu damar ganawa da musulmi, su tattauna don karfafa zumunci da hadin kan kasa.

Kara karanta wannan

An damke Soja yana baiwa masu garkuwa da mutane hayar bindiga AK-47

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Buru, wanda ya jagoranci fastoci da rabaran-rabaran fiye da 30 zuwa wurin taron ya taya Sarkin Musulmi, Alh. Abubakar Sa'ad da Sheikh Dahiru Bauchi, Sheikh Ibrahim El-Zakzakky, da Khalifa, Sanusi Lamido Sanusi na ɗariakar Tijanniyya murna.

Fastoci wurin Maulidi
Fastoci Sun Yi Bikin Maulidin Annabi SAW Tare Da Musulmi A Kaduna, Hotunansu Ya Kayatar. Hoto: Nigerian Tribune.
Asali: Facebook

A cewarsa:

"Sun zo wurin taron ne don karfafa kyawawan dangantaka tsakanin mabiya manyan addinan biyu (musulmi da kirista).
"Muna son samo hanyoyi masu kyau na inganta zaman lafiya da hakuri da juna tsakanin mabiya addinai daban-daban.
"Ya zama dole mu tuna cewa Allah kuda daya ya halicce mu, dukkan mu ƴaƴan Adamu da Hauwa'u ne, kuma muna da littafai masu tsarki (Bible da Kur'ani) daga Ubangiji guda daya don koyar da mu zaman lafiya da lumana da juna."

Buru ya nuna damuwa kan rashin tsaro a kasa musamman Arewa

Fasto Buru, amma, ya nuna damuwarsa kan kalluben tsaro a kasar musamman Arewa yana mai cewa zubar da jini, garkuwa, da hare-haren yan bindiga na shafar ilimi, noma, tattalin arziki, wasanni, yawon bude ido sauran bangarorin cigaban dan adam.

Kara karanta wannan

Tinubu ne zai ceto Najeriya: Jigon APC ya ce daga sama Allah ya zabi Tinubu ya gaji Buhari

Ya yi kira ga musulmi da kirista su fara yi wa kasar addu'a na musamman don samun tsaro.

Wakilan musulmi daga Jam'iyyar Nijar, Chadi, Senegal, Ghana, Sudan da Jamhuriyar Benin duk sun halarci taron Maulidin bana a Kaduna.

Hotunan Fasto Yana Raba Wa Almajirai Allo Da Kayan Karatu A Kaduna Don Bikin Ranar Zaman Lafiya Ta Duniya

A wani kokari karfafa hadin kai da zaman lafiya tsakanin addinai, cocin Christ Evangelical and Life Intervention Ministry ta raba wa dalibai alluna fiye da 100 a makaratun almajirai a Kaduna.

Yayin da ya jagoraci mambobin cocinsa a ranar Talata, Yohanna Buru, shugaban cocin, ya ce sun yi wannan karamcin ne don koyar da zaman lafiya, hakuri da addinai, da yan uwantaka tsakanin musulmi da kirista a jihar, rahoton The Cable.

Asali: Legit.ng

Online view pixel