An Kori Sanatan Adamawa da ya ki yarda Ya yi wa Tinubu Kamfe Daga Jam’iyyar APC

An Kori Sanatan Adamawa da ya ki yarda Ya yi wa Tinubu Kamfe Daga Jam’iyyar APC

  • Shugabannin APC na karamar hukumar Mubi ta Arewa sun bada sanarwar korar Elisha Ishiyahu Abbo
  • ‘Yan jam’iyyar ta APC sun fatattaki Sanata mai wakiltar Arewacin Adamawa bayan an yi bincike
  • Elisha Abbo ya ki yarda ya taya Bola Tinubu kamfe saboda ya dauki musulmi a matsayin abokin takara

Adamawa - Sanata mai wakiltar Arewacin jihar Adamawa, Elisha Abbo ya gamu da cikas a siyasa bayan korarsa daga jam’iyyar APC mai mulki.

Punch ta fitar da rahoto a karshen makon nan cewa shugabannin APC na karamar hukumarsa a jihar Adamawa, sun fatattaki Sanata Elisha Abbo.

Dalilin da shugabannin jam’iyyar na matakin karamar hukuma suka bada shi ne ana tuhumar ‘dan majalisar da yi wa jam’iyyarsa ta APC zagon-kasa.

Kara karanta wannan

Ba harka: Dan takarar shugaban kasan wata jam'iyya ya tsorata, zai janye daga takara

Sannan ana zargin Elisha Abbo da neman bata tsarin da ake bi wajen gudanar da siyasa a jam’iyyar.

Rahoto ya zo cewa a ranar Juma’a, shugabanni 13 da ke rike da jam’iyyar APC a jihar Adamawa suka sa hannu a takardar korar ‘dan majalisar dattawa.

A wani taron shugabannin APC na reshen karamar hukumar Mubi ta Arewa ne aka duba batun Sanata Abbo, aka tattauna a kai kafin a yanke hukunci.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sanata Elisha Abbo
Sanatan Adamawa ta Arewa, Elisha Abbo Hoto: dailypost.ng
Asali: Facebook

An yi aiki da rahoton kwamiti

Linda Ikeji ta kawo labarin, tana cewa majalisar shugabannin jam’iyyar sun duba rahoton kwamitin ladabtarwa wanda ya yi aiki a kan Sanatan.

Bayan la’akari da wannan rahoto ne aka yanke shawarar ayi waje da Abbo daga jam’iyyar APC, ana kafa hujja da hirar da ya yi da gidan talabijin AIT.

"Mutum 29 na kwamitin sun amince da rahoton kwamitin ladabtarwa na ranar 5 ga watan Oktoban 2022.

Kara karanta wannan

‘Yan Sanda Sun Sha Alwashin Tsamo Jami’ar da ta Rikewa Matar Atiku Jaka

Saboda haka mun kori Sanata Elisha Ishiyahu Abbo daga jam’iyya saboda hirar da ya yi da AIT yana suka da kushe ‘dan takaran shugaban kasar jam’iyya.”

- Jawabin 'yan jam'iyyar APC

Da aka tuntubi sakataren yada labarai na APC na jihar Adamawa, Mohammed Abdullahi, ya shaidawa ‘yan jarida maganar ba ta zo gare su ba tukun.

Tikitin Musulmi da Musulmi

Kafin daukar wannan mataki wannan Sanata ya fito fili yana cewa sam ba zai goyi bayan Asiwaju Bola Tinubu a zaben shugabancin kasa da za ayi a ba.

‘Dan siyasar yace a matsayinsa na daya daga cikin ‘ya ‘yan kungiyar Kiristoci ta CAN, ba zai iya mara baya ga tikitin Musulmi da Musulmi a Najeriya ba.

Abbo da wasu manyan 'yan siyasa irinsu Yakubu Dogara sun kuma halarci wani taron kiristocin Arewa inda aka ji labari an soki takarar Tinubu a APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel