‘Yan Sanda Sun Sha Alwashin Tsamo Jami’ar da ta Rikewa Matar Atiku Jaka

‘Yan Sanda Sun Sha Alwashin Tsamo Jami’ar da ta Rikewa Matar Atiku Jaka

  • Rundunar ‘yan sandan Najeriya (NPF) ta ce za ta dauki mataki akan jami’ar hukumar da ke kula da lafiyar Titi, matar Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar PDP
  • A ranar Laraba, dan takarar shugaban kasar na PDP, Atiku Abubakar, ya wallafa wasu hotunan matarsa a wani taro da aka yi a Abuja a shafinsa na Twitter
  • A daya daga cikin hotunan da aka wallafa, an ga wata jami’ar ‘yan sanda rike da jakar matar Atiku yayin da take yi wa jama’a jawabi a taron

Rundunar ‘yan sandan Najeriya (NPF) tana shirin daukar mummunan mataki akan jami’arsu da ke rike wa Titi, matar dan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar PDP jaka, jaridar The Cable ta rahoto.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun fusata, matar Atiku ta ba 'yar sanda ta rike mata jaka a wurin taro

Dan takarar shugaban kasar a ranar Laraba ya wallafa wasu hotunan matarsa a Twitter a wani taro da suka yi a Abuja.

Matar Atiku
‘Yan Sanda Sun Sha Alwashin Tsamo Jami’ar da ta Rikewa Matar Atiku Jaka. Hoto daga TheCable.ng
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kamar yadda ya wallafa a shafinsa:

“Taron S.H.E initiative daga matata, Hajia Titi Atiku Abubakar, ya kunshi abubuwa da dama da nafi so. Akwai harkar tsaro, lafiya da ilimi. Wadannan abubuwan guda uku su ne ke bai wa ko wanne mutum ‘yanci, musamman yara mata.”

A daya daga cikin hotunan an ga inda wata ‘yar sanda ke rike da jaka yayin da matar Atiku ke yi wa jama’a jawabi.

Wannan lamarin ya janyo cece-kuce a kafafen sada zumuntar zamani inda har ta kai ga ‘yan sanda sun kula.

Kakakin rundunar, Muyiwa Adejobi ya ce rike jaka ba aikin dan sanda bane.

“Ba za mu lumunci hakan ba. Mun fara daukar matakan da su ka dace. Kuma sai mun nemota,” a cewar Adejobi.

Kara karanta wannan

Majiya Ta Bayyana Ranar Dawowar Tinubu Najeriya, Zai Halarci Wani Muhimmin Taro A Abuja

“An tuntubi shashin AIG Special Protection don su taimaka mana wurin gano ‘yar sandar. A hankali za mu kawo gyara akan lamarin.”

A ‘yan kwanakin nan, sanya ‘yan sanda a matsayin masu kulawa da lafiyar manyan mutane yana ta janyo cece-kuce iri daban-daban.

A watan Satumba, an kama Zainab Duke-Abiola, wata farfesa kuma mai rajin kare hakkin bil’Adama bisa zarginta da cutar da Teju Moses, wata sifetar ‘yan sanda.

Atiku ya sha alwashin mikawa ‘yan kabilar Ibo shugabanci bayan wa’adin mulkinsa

A wani labari na daban, ‘Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya ce ‘yan kabilar Igbo za su iya zama shugaban kasa ne kawai bayan ya kammala wa’adin mulkinsa.

Atiku ya kuma sha alwashin bayar da fifikon ayyukan raya kasa a yankin Kudu maso Gabas da sauran yankuna idan aka zabe shi a 2023, yana mai cewa duk wani aiki da aka yi a kowacce jiha alheri ne ga Najeriya baki daya.

Kara karanta wannan

Hotunan Sauran Fasinjoji 23 na Jirgin Kasan Abj-Kd da Suka yi Kwana 192 Hannun ‘Yan Ta’adda

Atiku, wanda ke jawabi ga masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP na Kudu maso Gabas a jihar Enugu ranar Talata, ya ce:

“Ni ne matakalar da ‘yan kabilar Igbo za su iya bibiya don zama shugaban Najeriya”.

Asali: Legit.ng

Online view pixel