Abin da Zai Jawo Kotu Ta Iya Hana Bola Tinubu da Sauran ‘Yan APC Tsayawa Takara

Abin da Zai Jawo Kotu Ta Iya Hana Bola Tinubu da Sauran ‘Yan APC Tsayawa Takara

  • Mai shari’a Emeka Nwite ya rusa shiga takarar Isiaka Oyetola da Mataimakinsa a zaben jihar Osun
  • Kotu tace bai kamata Gwamna Isiaka Oyetola ya tsaya takara ba saboda Mai Mala Buni ya kai sunansa
  • Idan kotu ta tabbatar da bata ayyukan da Mala Buni ya yi, za a iya rusa APC NWC da ‘yan takaran 2023

Abuja - APC ta damu da hukuncin da babban kotun tarayya mai zama a Abuja tayi na ruguza tsaida Isiaka Oyetola a matsayin ‘dan takarar Gwamnan Osun.

Rahoton Tribune yace ‘Ya ‘yan jam’iyyar APC su na jin tsoron wannan hukunci da Alkali ya yi a kan Isiaka Oyetola da mataimakinsa su shafi zaben 2023.

Kotu tace shiga takararsu Isiaka Oyetola a zaben Gwamnan Osun ya ci karo da doka da tsarin mulki domin Mai Mala Buni ne ya mikawa INEC sunayensu.

Kara karanta wannan

Yadda Sowore Ya Kusa Yin Fada da Hamza Al-Mustafa da Kashim Shettima a Taro

Hukuncin da Alkali ya zartar shi ne dokar zabe da sashe na dokar kasa na 183 sun ce Buni bai isa ya rike kujerar shugaban jam’iyya alhali yana gwamna ba.

'Yan takara sun shiga garari

Gwamnan jihar Osun ya yi alkawarin zai daukaka kara domin ayi watsi da wannan hukunci. Jaridar Sunday Tribune tace cikin ‘yan takara ya duri ruwa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Idan hukuncin Mai shari’a Emeka Nwite ya zauna, duk wani ‘dan takaran jam’iyyar APC da Mala Buni ya gabatarwa INEC sunansa, yana fuskantar barazana.

Yan APC
Bola Tinubu suna kamfe a Ekiti Hoto: www.vanguardngr.com
Asali: UGC

Daga cikin ayyukan da gwamnan na Yobe yayi yana rike da kujerar shugabancin APC na rikon kwarya akwai ba Abiodun Oyebanji tikiti a zaben jihar Ekiti.

Bugu da kari shi ya gudanar da zaben shugabannin jam’iyya na kasa har aka nada majalisar NWC. Za a samu makamancin wannan rahoto a shafin Nairaland.

Kara karanta wannan

Ohanaeze Ndigbo Sun yi wa Atiku Martani Kan Ikirarin Zai Mikawa Ibo Shugabancin Kasa

Su kuma ‘yan majalisar gudanarwa na NWC ne suka shirya zaben fitar da gwanin da ya ba Bola Tinubu damar zama ‘dan takaran shugabancin Najeriya a 2023.

APC ta dabawa kanta wuka

Wani lauya masanin tsarin mulki, Dr Kayode Ajulo ya shaidawa jaridar cewa APC ce ta jefa kanta a rami, domin ba ta saurari shawararsa a kan Mala Buni ba.

Dr Kayode Ajulo yace idan aka bi hukuncin babban kotun, dole a ruguza shugabannin APC, wanda hakan zai iya jawo ‘yan takaran zaben 2023 su rasa tikitinsu.

Mr Felix Morka wanda ke magana da yawun bakin jam’iyya na kasa yace kotun daukaka kara za ta canza hukunci domin Emeka Nwite ya tafka kuskure.

SGF bai goyon bayan Tinubu?

Farfesa Tahir Mamman ya yi jawabi yana mai karyata rade-radin cewa SGF yana goyon bayan PDP a 2023 saboda an gan shi a gidan Alhaji Atiku Abubakar.

Mamman yace Boss Mustapha yana marawa Bola Tinubu baya ya karbi mulki a zabe mai zuwa, yace ta'aziyya ta kai SGF zuwa gidan Atiku domin 'dan jiharsu ne.

Kara karanta wannan

An fara kamfe: Atiku Ya Dura Abuja, Tinubu Ya Tafi Landan, Peter Obi Ya Dakata Tukun

Asali: Legit.ng

Online view pixel