Yadda Sowore Ya Kusa Yin Fada da Hamza Al-Mustafa da Kashim Shettima a Taro

Yadda Sowore Ya Kusa Yin Fada da Hamza Al-Mustafa da Kashim Shettima a Taro

  • ‘Dan takarar shugaban kasa a inuwar African Action Congress ya yi takaddama da takwarorinsa na 2023 a taro
  • Omoyele Sowore ya yi cacar baki da Kashim Shettima da ya halarci taron sa hannu a yarjejeniyar zaman lafiya
  • An ji Sowore yana surutu da Manjo Hamza Al-Mustapha wanda shi ma yake neman takarar shugaban kasa

Abuja - An yi ‘yar karamar hayaniya a lokacin da ‘yan takarar shugaban kasa suka je sa hannu a yarjejeniyar zaman lafiya a zaben da za ayi a 2023.

Rikici ya nemi ya kaure ne yayin da Kashim Shettima ya zauna a kujerar da aka warewa ‘dan takarar shugaban kasa, alhali shi abokin takara ne.

Ganin Sanata Kashim Shettima a sahun gaba bai yi wa Yele Sowore dadi ba, hakan ta sa ya kalubalanci ‘dan takaran mataimakin shugaban kasar.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Tinubu ya ce zai ba 'yan Najeriya mamaki, zai sauya makomar Najeriya

Yayin da shi Sowore ya samu kansa a kujerar baya, shi kuwa Shettima ya samu kujera a gaba, yana mai wakiltar ‘dan takaran APC, Bola Tinubu.

‘Dan gwagwarmayar yana ganin bai kamata tsohon gwamnan na Borno ya zauna a gaban shi ba domin kuwa Tinubu ne yake rike da tutar APC.

A wani bidiyo da Sowore ya wallafa a shafinsa, an ji yana cewa bai dace Tinubu ya rika neman takarar shugaban kasa ta hanyar aiko wakilci ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Omoyele Sowore
Omoyele Sowore a taron da aka shirya Hoto: @YeleSowore
Asali: Twitter

Meya kai Shettima sahun gaba?

“Wannan bai nufin ba zan cigaba da magana ba, wannan shi ne matsaya ta a kan zamansa a gaba. Na tunkare shi, nace meyasa yake zama a nan tun da Tinubu ba ya nan.”
“Da ni na ke zauna a can, ba zan tashi ba saboda Tinubu ya kamata ya zauna a wurin, ba shi (Shettima) ba. Ba zai yiwu ka rika takara alhali ba ka nan ba.”

Kara karanta wannan

2023: Nasihar da Shugaba Buhari Ya Yi Wa Yan Takarar Shugaban Kasa 18 a Wurin Taron Abuja

- Omoyele Sowore

Sai kuma Manjo Hamza Al-Mustapha

Ana gama wannan sai ga ‘dan takara na AAC yana cacar baki da Manjo Hamza Al-Mustapha mai ritaya wanda ya yi aiki da Marigayi Janar Sani Abacha.

Hamza Al-Mustapha ya fadawa Sowore cewa akwai bambanci a tsakaninsu, inda tsohon ‘dan jaridar yake cewa shi ne wanda ya tsaya a kan gaskiya.

Sowore ya fadawa tsohon sojan cewa a lokacin da shi da Janar Abacha suke ta’adi, shi kuma a matsayin jagoran dalibai, ya tsayawa hakkin al’umma.

Meyasa Tinubu ya tafi Landan?

A ranar Juma’a aka ji labari Ayo Oyalowo yace Bola Tinubu ya bar Najeriya ne da nufin ya samu lokacin hutu, domin a Legas da Abuja, ba zai sarara ba.

Daya daga cikin ‘yan kwamitin yakin neman zaben APC a 2023 yace ‘dan takaran na su yana aikin awanni 20 a kullum yaumin, don haka dole ne ya huta.

Kara karanta wannan

2023: Tinubu Ba Zai Samu Damar Sa Hannu Kan Wata Muhimmiyar Takarda ba

Asali: Legit.ng

Online view pixel