Jigon APC Ya Wanke Wanda Ake Zargi da Goyon Bayan Atiku a Fadar Shugaban kasa

Jigon APC Ya Wanke Wanda Ake Zargi da Goyon Bayan Atiku a Fadar Shugaban kasa

  • Tahir Mamman ya yi jawabi yana mai karyata rade-radin da ke yawo cewa SGF yana goyon bayan PDP
  • Farfesa Mamman yake cewa Boss Mustapha yana marawa Bola Tinubu baya ya karbi mulki a zaben 2023
  • Lauyan yace babu zaman kasan da SGF ke yi domin hana Tinubu zama magajin Muhammadu Buhari

Abuja - Farfesa Tahir Mamman wanda yana cikin kusoshi a jam’iyyar APC, ya wanke Boss Mustapha daga zargin da ake yi masa na goyon bayan Atiku Abubakar.

The Cable tace ana yada jita-jita Sakataren gwamnatin tarayya mai-ci, Boss Mustapha yana tare da ‘dan takaran PDP, Alhaji Atiku Abubakar a zabe mai zuwa.

A cikin makon nan, aka rika yada wannan labari saboda an ga Mustapha ya kai wa Wazirin Adamawa Atiku ziyara domin yi masa ta’aziyyar rashin wani hadiminsa.

Kara karanta wannan

Kan ku ake ji: Atiku Abubakar Ya Maida martani ga 'Yan PDP da Ake Rikici da su

Ganin Abdullahi Nyako ya rasu, sai Sakataren gwamnatin tarayyan a matsayinsu duk na mutanen Adamawa, ya yi wa ‘dan takaran shugabancin kasar ta’aziyya.

Mamman yace wannan labari bai da tushe ko makama, yake cewa Boss Mustapha yana tare da APC, kuma zai taimakawa jam’iyya mai-mulki wajen lashe zabe.

Boss Mustapha da Atiku
Boss Mustapha a gidan Atiku Abubakar Hoto: @Rasheethe
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jawabin Tahir Mamman

“Hankalinmu ya zo ga wani labari na karya cewa sakataren gwamnatin tarayya (SGF), Mr. Boss Mustapha, babban hadimin Muhammadu Buhari (GCFR), ana tuhumarsa da yi wa ‘dan takaran PDP, Alhaji Atiku Abubakar aiki.
...a maimakon ya goyi bayan ‘dan takaran jam’iyyarsa mai mulki, All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Duk da mun fahimci ana lokacin siyasa ne inda ake ganin tarkace, amma wannan labari bai da tushe, sharri ne, ba haka abin yake ba.
“A matsayin wanda ya yi aiki kusa-da-kusa da SGF a lokacin kwamitinmu na CECC, kuma har yanzu ina tare da shi, mu na aiki a jam’iyyance.

Kara karanta wannan

Yadda Atiku Zai Bi Wajen Maganin Akidar Biyafara Da Tayi Shekara da Shekaru

Zan iya aron bakinsa in tauna masa albasa a kan wannan batu. SGF 'dan jam’iyya ne wanda yake da karfi sosai a matakan jiha da kasa.
“Ya nuna jajircewa wajen taimakawa manufar APC da akidar Muhammadu Buhari (GCFR). Wannan ya sa yake tare da ‘dan takaran APC, Bola Tinubu.

A karshe, Guardian ta rahoto Mamman yana cewa bai kamata ayi amfani da ziyarar da SGF ya kai wa Wazirin Adamawa a matsayin zama na siyasa ba.

Rigimar Wike da Atiku

Kafin nan mun ji Gwamnan Ribas watau Nyesom Wike ya fito yana ikirarin akwai wani a fadar shugaban kasa da ke marawa PDP baya a babban zaben 2023.

An kuma rahoto Nyesom Wike ya lashi takobin tona asirin wasu shugabannin jam'iyyar PDP masu ikirarin su iyayen jam'iyyar ne da ke neman yakarta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel