Ohanaeze Ndigbo Sun yi wa Atiku Martani Kan Ikirarin Zai Mikawa Ibo Shugabancin Kasa

Ohanaeze Ndigbo Sun yi wa Atiku Martani Kan Ikirarin Zai Mikawa Ibo Shugabancin Kasa

  • Kungiyar Ohanaeze Ndigbo ta yi wa Atiku martani bayan ya ce idan ya kammala wa'adin mulkinsa zai mika ragamar kasar Najeriya hannun Ibo
  • Kamar yadda Ohanaeze suka ce, ikirarin Atiku abun dariya ne saboda tuni suka hango yadda Peter Obi Zai yi caraf da mulkin kasar a 2023
  • Ndigbo ta yi dogaro da dukkan zabukan da aka yi ta yanar gizo wanda ya nuna yadda Obi ya lallasa Atiku, kuma sun ce hakan zai faru

Kungiyar kololuwa ta kabilar Ibo, Ohanaeze Ndigbo a jiya ta zakulo maganar da ‘dan takarar jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar yayi inda yake ikirarin cewa shi ne zai kasance tsanin da zai kai Ibo shugabancin kasa inda suka kwatanta batun da abin dariya.

A cikin kwanakin nan ne Atiku ya ziyarci Enugu inda ya hana da manyan masu ruwa da tsakin yankin tare da cewa shugabancin kasa na kabilar Ibo zai zo ne daga wurin shi bayan ya kammala wa’adin mulkinsa, jaridar Guardian ta rahoto.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Tinubu ya ce zai ba 'yan Najeriya mamaki, zai sauya makomar Najeriya

Ohanaeze Ndigbo
Ohanaeze Ndigbo Sun yi wa Atiku Martani Kan Ikirarin Zai Mikawa Ibo Shugabancin Kasa. Hoto daga guardian.ng
Asali: UGC

Amma Ohanaeze a wata takardar da suka saki a Abakaliki ta hannun babban sakatarensu, Okechukwu Isiguzoro, sun tuhumi Atiku ta kan ikirarin da yayi kan cewa ta yaya zai kasance tsanin Ibo bayan tuni ‘yan Najeriya suke goyon bayan Peter Obi domin karbar ragamar kasar nan a zaben 2023 mai gabatowa.

Ya jaddada cewa, dukkan zabukan da aka yi a yanar gizo sun bayyana cewa Obi ne ke dauke da nasara ba wai a matsayinsa na ‘dan takarar shugaban kasa na Ibo ba, sai dai matsayin mai hada kan dukkan yankunan kasar nan.”

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Takardar ta ce:

“Ohanaeze na son sanar da cewa, maganar Atiku, ‘dan takarar shugabancin kasa na PDP a Enugu a kwanaki biyu da suka gabata na cewa shi zai zamo tsanin shugabancin kasa na Ibo abun dariya ne.
“Ta yaya Atiku zai yi wannan ikirarin ga ‘yan Najeriya bayan kusa dukkan kabilu suna bayan Peter Obi don ya shugabanci kasar nan a 2023 babu dogaro da kabila, sai dai zai wakilci zabin sabuwar Najeriya."

Kara karanta wannan

2023: Tinubu Ba Zai Samu Damar Sa Hannu Kan Wata Muhimmiyar Takarda ba

Atiku Yace 'Yan Kabilar Ibo Zai Mikawa Mulki Idan Ya Kammala Wa'adinsa

A wani labari na daban, Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya ce ‘yan kabilar Igbo za su iya zama shugaban kasa ne kawai bayan ya kammala wa’adin mulkinsa.

Atiku ya kuma sha alwashin bayar da fifikon ayyukan raya kasa a yankin Kudu maso Gabas da sauran yankuna idan aka zabe shi a 2023, yana mai cewa duk wani aiki da aka yi a kowacce jiha alheri ne ga Najeriya baki daya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel