2023: Nan Babu Dadewa Wike da Tawagarsa Zasu Koma Wurin Tinubu, 'Dan APC Yayi Hasashe

2023: Nan Babu Dadewa Wike da Tawagarsa Zasu Koma Wurin Tinubu, 'Dan APC Yayi Hasashe

  • Tsohon 'dan takarar shugaban matasan APc na kasa, Ahmad Abba Dangata, ya yi hasashen cewa Gwamna Wike da tawagarsa zasu yi wa Tinubu aiki
  • Dangata ya sanar da hakan a tattaunar da yayin da Legit.ng a yayin da Najeriya ke shirin fara gangamin zaben 2023
  • Matashin jigon APC din ya yi magana kan irin rawar da Atiku da Peter Obi zasu taka a zaben shugabancin kasa na 2023

A yayin da rikicin cikin gida ke cigaba da kamari a jam'iyyar PDP ta hamayya, tsagin Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas sun janye daga tawagar gangamin zaben shugabancin kasa.

Duk da Gwamna Wike, shugaban tsagin, yace ba zai bar jam'iyyar PDP ba, akwai hasashen dake nuna cewa shi da mukarrabansa zasu yi wa Tinubu aiki.

Kara karanta wannan

Hotunan Motar Kudin Banki Da Ta Kama Da Wuta Tsakiyar Titi A Kebbi

Abba Dangata
2023: Nan Babu Dadewa Wike da Tawagarsa Zasu Koma Wurin Tinubu, 'Dan APC Yayi Hasashe
Asali: Facebook

Ana tsaka da wannan hasashen, Legit.ng ta zanata da Ahmad Abba Dangata, tsohon mai neman takarar shugaban matasa na kasa na jam'iyyar APC wanda ya bayyana tunaninsa kan wannan cigaban da sauran abubuwan da suke yawo a jam'iyyar.

Dalilin da yasa Wike da Tsaginsa Ka Iya yi wa Tinubu aiki

Da aka tambaya idan Wike da tawagarsa zasu goyi bayan Tinubu bayan sun janye daga tawagar kamfen din Atiku, Dangata yace:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Tabbas, ina tunanin Wike da tawagarsa zasu goyi bayan Tinubu."

Haifaffen jihar Kano din kuma jigon APC yace Gwamna Wike da tawagarsa sun sakankance wurin goyon bayan kwararren 'dan takara, inda ya kara da cewa:

"Tinubu yana da dukkan nagartar da ake bukata. Don haka nan babu dadewa Wike da tawagarsa zasu hade da Tinubu."

Atiku ba Zai iya Nasara ba, koda Wike ya Goyi bayansa

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Hotuna Sun Bayyana A Yayin Da Peter Obi Ya Kaddamar Da Kamfen Dinsa A Babban Jihar Arewa

'Dan takara shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, yana daya daga manyan masu barazana a takarar shugaban kasa a shekarar 2023.

Jama'a da yawa sun yarda cewa yana da babban rabo idan ya iya janyo Gwamna Wike da tawagarsa zuwa bangarensa.

Sai dai Dangata, yace 'dan takarar jam'iyyar APC na kasa, Bola Ahmed Tinubu zai lallasa Atiku idan har ya iya janyo Wike bangarensa.

"Ko da goyon bayan Wike ko babu goyon bayansa, Atiku ba inda zai kai. Ba zai ma iya yin nasara a yankin arew amasi gabas ba balle kuma Najeriya baki daya.
"A halin da ake ciki yanzu, Najeriya da 'yan Najeriya na bukatar mutum kamar Tinubu. Kuma 'yan Najeriya sun yanke hukuncin zaben Tinubu."

An Gano Yadda Tinubu Ya Assasa Rikicin APC kan Kwamitin Yakin Neman Zabensa

A wani labari na daban, manyan alamu na nuna cewa mai 'dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu, ya shuka sabuwar rigima a kwamitin yakin neman zabensa na shugaban kasa (PCC) bayan ya zagaye shugaban kasa Muhammadu Buhari, shugabancin jam'iyya da gwamnonin jam'iyyar wurin kafa kwamitin.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Machina Ya Kada Ahmad Lawan A Kotu, An Alantasa Matsayin Sahihin Dan Takara

Jaridar Thisday ta rahoto cewa, sassa uku ne aka tsara wanda ya hada da 'dan takarar shugaban kasa, jam'iyya da shugaban kasa wadanda zasu samu jagorancin gwamnoni tunda su ne zasu jagoranci yakn nemen zaben a jihohinsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel