Zaben 2023: Hotuna Sun Bayyana A Yayin Da Peter Obi Ya Kaddamar Da Kamfen Dinsa A Babban Jihar Arewa

Zaben 2023: Hotuna Sun Bayyana A Yayin Da Peter Obi Ya Kaddamar Da Kamfen Dinsa A Babban Jihar Arewa

  • Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party, Peter Obi, ya dira Jos, babban birnin jihar Plateau don gangamin siyasa
  • Gangamin shine na farko da dan takarar shugaban kasar zai halarta da kansa tunda magoya bayansa suka fara yin gangami dominsa
  • An hangi dan takarar shugaban kasar tare da abokin takararsa, Datti Baba-Ahmed, a hotuna a ranar Laraba, 28 ga watan Satumba, wanda shine ranar da INEC ta tsayar a hukumance na fara kamfen din zaben shugaban kasa na 2023

Jos, Plateau - A yayin da aka fara kamfen din zaben shugaban kasa na shekarar 2023 a Najeriya, Labour Party da dan takarar shugaban kasarta sun kaddamar da kamfen dinsu a Jos, babban birnin Jihar Plateau.

An hangi Peter Obi da abokin takararsa, Yusuf Datti Baba-Ahmed, a wasu hotuna masu kayyatarwa da The Nation ta wallafa a Twitter.

Kara karanta wannan

Babu Banbanci Tsakanin Obi, Atiku Da Tinubu, In Ji Kachikwu, Dan Takarar Shugaban Kasa Na ADC

Peter Obi a Jos.
Zaben 2023: Hotuna Sun Bayyana A Yayin Da Peter Obi Ya Kaddamar Da Kamfen Dinsa A Babban Jihar Arewa. Hoto: @TheNationOnline.
Asali: Facebook

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Peter Obi na daya daga cikin manyan yan takarar shugaban kasa a zaben na 2023 kuma yana da magoya baya sosai musamman a intanet.

Tsohon gwamnan na Jihar Anambra ya yi nasara a zaben jin ra'ayi da aka yi don hasashen wanda zai yi nasara a zaben.

Amma, an soki zaben jin ra'ayin da dalilai da yawa ciki har da cewa mafi yawancin masu zabe ba su dandalin sada zumunta.

Ka Ja Kunnen Magoya Bayan Ka, Tinubu Ya Gargadi Peter Obi Kan Yada Labaran Karya

A wani rahoton, Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Bola Tinubu, ya bukaci takwararsa na Labour Party, Mr Peter Obi, ya ja kunnen magoya bayansa don su dena yada karya, makirci da aibanta shi da sauran yan takara.

Kara karanta wannan

Chimaroke Nnamani: Sanatan PDP Da Aka Sunansa A Kwamitin Kamfen Din Tinubu Ya Yi Martani, Ya Faɗa Jam'iyyar Da Zai Yi Wa Kamfen

Tinubu, cikin sanarwar da direktan watsa labaransa, Mr Bayo Onanuga ya fitar, ya bukaci Obi ya ja kunnen magoya bayansa kuma ya bari zaben 2023 ya zama kan batutuwan da za su bunkasa kasa, cigaba da kwanciyar hankalin Najeriya, yana gargadin "karya da yada maganganu marasa tushe za ba su saka a ci zabe ba."

Ya ce zaben kasar za ta yi armashi idan aka mayar da hankali wurin batutuwan da za su inganta rayuwar yan Najeriya da fito da su daga talauci a maimakon shirme irin na yan tasha wadanda ba su nufin kasar da alheri.

Asali: Legit.ng

Online view pixel