Kotu Ta Alanta Machina Matsayin Sahihin Dan Takarar Sanatan Yobe, Ta Yi Watsi Da Ahmad Lawan

Kotu Ta Alanta Machina Matsayin Sahihin Dan Takarar Sanatan Yobe, Ta Yi Watsi Da Ahmad Lawan

Babbar kotun tarayya dake zamanta a Damaturu, birnin jihar Yobe ta raba gardama tsakanin Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, da Hanarabul Bashir Machina.

Kotun ta umurci uwar jam'iyyar All Progressives Congress (APC) da Hukumar INEC su gaggauta sanya sunan Bashir Machina matsayin sahihin dan takaran kujerar Sanata mai wakiltar Yobe Ta Arewa a zaben 2023.

Alkali Fadima Murtala Aminu ta umurci APC ta tura sunan Machina wajen INEC saboda shi ya lashe zaben fidda gwanin ranar 28 ga Mayu, 2022, rahoton TheNation.

Alkalin tace zaben da Shugaban Majalisar dattawa Ahmad Lawan ke ikirarin yayi nasara ta bogi ce.

Machina
Kotu Ta Alanta Machina Matsayin Sahihin Dan Takarar Sanatan Yobe, Ta Yi Watsi Da Ahmad Lawan
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel