An Gano Yadda Tinubu Ya Assasa Rikicin APC kan Kwamitin Yakin Neman Zabensa

An Gano Yadda Tinubu Ya Assasa Rikicin APC kan Kwamitin Yakin Neman Zabensa

  • Alamu sun bayyana yadda Bola Ahmed Tinubu da kansa ya assasa wutar dake tashi a jam'iyyar APC kan jerin sunayen 'yan kwamitin kamfen dinsa
  • Kamar yadda aka gano, Tinubu duk da shawarar da ya samu daga Buhari, shugabannin jam'iyyar da gwamnoni, yayi watsi da su yayi komai gaban kansa
  • Manyan masu ruwa da tsakin da zasu bashi kariya duk da cece-kucen da tikitin Musulmi da Musulmi ya janyo duk yayi watsi da su

Manyan alamu na nuna cewa mai 'dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu, ya shuka sabuwar rigima a kwamitin yakin neman zabensa na shugaban kasa (PCC) bayan ya zagaye shugaban kasa Muhammadu Buhari, shugabancin jam'iyya da gwamnonin jam'iyyar wurin kafa kwamitin.

Jaridar Thisday ta rahoto cewa, sassa uku ne aka tsara wanda ya hada da 'dan takarar shugaban kasa, jam'iyya da shugaban kasa wadanda zasu samu jagorancin gwamnoni tunda su ne zasu jagoranci yakn nemen zaben a jihohinsu.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Shugaba Buhari ya bayyana yadda sabbin shugabannin za su samu

Don haka, a cewar majiyoyi, Tinubu, jam’iyyar da gwamnonn, sun kammala kafa kwamitin yakin neman zabe, kafin a amince da su a kai wa shugaban kasa jerin sunayen da ya ba shi shawara a matsayin alamar girmamawa, an ce Buhari bai yi maraba da sunayen ba, har ya yi kamar yadda ake tsammani daga gare shi ta hanyar yin ƴan bayanai.

Sai dai kuma kwanaki kadan da shugaban kasa ya yi tsokaci, Tinubu, ba tare da neman ko daya daga cikin wadanda suka dace ba har da Buhari, ya duba jerin sunayen shi daya ya fitar da su.

Wannan, ana tsammanin, ya haifar da damuwa a cikin jam'iyyar har da tsakanin sauran masu ruwa da tsaki.

Har ila yau, a yankin Kudu maso Yamma, an ce gwamnonin sun dauki Gwamnan Jihar Ekiti, Kayode Fayemi, a matsayin kodinetan PCC na shiyyar, amma Tinubu ya ki amincewa da zabinsu, kuma a madadinsa, ya gwammace Gwamnan Jihar Ondo, Oluwarotimi. Akeredolu, SAN ya kasance kodinetan.

Kara karanta wannan

Atiku Yace 'Yan Kabilar Ibo Zai Mikawa Mulki Idan Ya Kammala Wa'adinsa

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Baya ga hakan, tuni akwai cece-kucen da ake ta yi na tikitin Musulmi da Muslumi wanda masu ruwa da tsaki suka sakankance cewa dauko Kirista daya Binuwai zai matukar yin amfani wurin kwantar da wutar da ke tashi idan aka saka 'dan nan matsayin sakataren kwamitin.

An gano cewa, an aikewa da Tinubu sunayen kiristoci biyu daga Binuwai don ya duba tare da sanya daya daga cikin matsayin sakataren kwamitin kamfen din amma yayi burus.

A yayin da shugaban kasa ya ki magana kan wannan lamarin, wasu 'yan siyasan sun dinga yi masa magana da ya gyara wannan jerin sunayen kada ya bari hakan ya bata siyasarsa.

An Gargadi Tinubu Kan Shirinsa Na Amfani da Kudi Wajen Raba Kawunan Kiristoci a Zaben 2023

A wani labari na daban, an gargadi jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da dan takarar shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, kan amfani da kudi wajen kawo rabuwar kai tsakanin Kiristoci.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari Ya Fadi Gaskiya Kan Kishin-Kishin Din Ya Nemi a Tube Keyamo Daga Kamfen Din Tinubu

Gargadin na kunshe ne a cikin wata sanarwa daga kungiyar dattawan Kirista a jihohin arewa, dauke da sa hannun shugabanta, Oyinehi Inalegwu, a ranar Talata, 27 ga watan Satumba, jaridar Punch ta rahoto.

Sanarwar ta ce:

“Mun gargadi APC da ta daina amfani da kudi don dauka da haddasa rabuwar kai a tsakanin Kiristoci, musamman a arewa."

Asali: Legit.ng

Online view pixel