2023: Ba Zan Bari 'Ya'Ya Na Sun Tafi Kasashen Waje Ba, Atiku Ya Dauki Wasu Alkawurra

2023: Ba Zan Bari 'Ya'Ya Na Sun Tafi Kasashen Waje Ba, Atiku Ya Dauki Wasu Alkawurra

  • Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace ba zai bar 'yayansa su koma wata ƙasa da zama ba komi wahala
  • Mai neman zama shugaban kasa a inuwar PDP ya ɗauki alƙawurra ga 'yan Najeriya yayin taronsa da kusoshin PDP a Enugu
  • A ranar 28 ga watan Satumba, 2022, za'a fara yaƙin neman zaɓen zama shugaban ƙasa a hukumance

Enugu - Ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, yace duk da wahalhalun da ake sha a mulkin APC, ba zai bari 'ya'yan da ya haifa su bar Najeriya zuwa wata ƙasa ba.

Vanguard ta ruwaito cewa Atiku ya yi wannan furucin ne a wurin ganawarsa da masu ruwa da tsakin jam'iyyar PDP na kudu maso gabas a jihar Enugu ranar Talata.

Kara karanta wannan

Atiku Yace 'Yan Kabilar Ibo Zai Mikawa Mulki Idan Ya Kammala Wa'adinsa

Alhaji Atiku Abubakar.
2023: Ba Zan Bari 'Ya'Ya Na Sun Tafi Kasashen Waje Ba, Atiku Ya Dauki Wasu Alkawurra Hoto: thecable
Asali: UGC

Haka zalika Atiku ya tabbatar da cewa zai maida hankali wajen cigaban al'umma da inganta ilimi domin ba matasa dama su yi gogayya a tattalin arziƙin zamani.

A kalamansa kamar yadda The Cable ta ruwaito, Atiku yace:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"A gwamnatin mu ta baya da nake mataimakin shugaban ƙasa, kun ga yadda yan Najeriya ke gudo wa daga kasashen waje suna dawowa gida don zuba hannun jarinsu lokacin akwai damarmaki, ni na shaida haka a jami'ata."
"Lokacin da na tabbatar da tsarin da zai gogayya da na ƙasa da ƙasa, da yawan yan Najeriya daga Amurka da ƙasahen Turai gida suka dawo ba wai Legas ko Abuja kaɗai ba har da Yola, arewa maso gabas."
"Duk sun dawo, abinda zamu yi kawai shi ne mu tabbatar ƙasar mu ta kai matakin da zata jawo hankalinsu su dawo kuma tabbas za su dawo. A mulkin APC abin ya juya, mutane sun ƙagara su fita Najeriya."

Kara karanta wannan

2023: Ɗan Takarar Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, Ya Dira Jihar Enugu, Zai Gana da Kusoshin PDP

Na hana 'Ya'yana zuwa ko ina - Atiku

Tsohon mataimakin shugaban ƙasan yace da yawan mutane sun bar 'yan uwansu ko 'ya'yansu sun gudu daga mahaifarsu Najeriya amma bai bar iyalansa ba.

"Da yawanku nan kuna da 'yan uwa da 'ya'ya, waɗanda suka sa ƙafa suka gudu zuwa Amurka ko Kanada. Ni ma ina da nawa amma na hana ko ɗaya ya tafi ƙasar waje ya zauna domin ban yarda ba."

Zamu inganta ɓangaren lafiya - Atiku

Bugu da ƙari, Atiku ya ɗauki wasu alƙawurra da suka haɗa da cewa zai tabbatar a inganta wuraren neman lafiyar mutane idan ya zama shugaban kasa.

"Haka nan zamu samar da tsarin kula da lafiya mai kyau da inganci. Saboda haka zamu zuba hannun jari mai tsoka a ɓangaren. Ingantaccen ilimi da lafiyar ma'aikata na da matuƙar amfani ga tattalin arziki da bunƙasar dukiya a duniyar yau."

- Atiku Abubakar.

A wani labarin kuma mun tattara muku Jerin Kasuwanci 6 da Zasu Amfana da Yaƙin Neman Zaben Shugaban Kasa 2023

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Halaka Babban Ɗan Sanda, Sun Yi Garkuwa da Matafiya a Jihar Buhari

A yau Laraba, 28 ga watan Satumba, 2022 jam'iyyu zasu kaɗa gangar yaƙin neman zaɓe domin tunkarar babban zaɓen 2023 kamar yadda hukumar INEC ta tsara a jadawalinta.

Najeriya zata shaida manyan harkokin kamfe waɗanda ka iya taɓa tattalin arzikin kasa. A zaɓen da ya wuce 2019 an ƙayyade iyakar kudin da kowace jam'iyya zata iya kashe wa Biliyan ɗaya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel