Atiku Yace 'Yan Kabilar Ibo Zai Mikawa Mulki Idan Ya Kammala Wa'adinsa

Atiku Yace 'Yan Kabilar Ibo Zai Mikawa Mulki Idan Ya Kammala Wa'adinsa

  • Alhaji Atiku Abubakar, 'dan takarar kujerar shugabancin kasa na jam'iyyar APC, yace Ibo zai mikawa mulkin Najeriya idan ya kammala wa'adinsa
  • Ya sanar da cewa zai bai wa yankin kudu maso gabashin Najeriya fifiko hatta a yayyukan cigaba da more rayuwa ta 'yan Najeriya
  • Atiku yace abun takaici ne yadda gwamnatin shugaba Buhari tayi watsi da yankin duk da cigaban yankin na Najeriya ne baki daya

Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya ce ‘yan kabilar Igbo za su iya zama shugaban kasa ne kawai bayan ya kammala wa’adin mulkinsa.

Atiku ya kuma sha alwashin bayar da fifikon ayyukan raya kasa a yankin Kudu maso Gabas da sauran yankuna idan aka zabe shi a 2023, yana mai cewa duk wani aiki da aka yi a kowacce jiha alheri ne ga Najeriya baki daya.

Kara karanta wannan

Bayan Atiku Ya Kammala Wa'adin Mulkiinsa, Kudu Maso Gabas Ce Zata Samar da Shugaban Kasa, Jigon PDP

Atiku da Ibo
Atiku Yace 'Yan Kabilar Ibo Zai Mikawa Mulki Idan Ya Kammala Wa'adinsa. Hoto daga thenationonlineng.net
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Atiku, wanda ke jawabi ga masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP na Kudu maso Gabas a jihar Enugu ranar Talata, ya ce:

“Ni ne matakalar da ‘yan kabilar Igbo za su iya bibiya don zama shugaban Najeriya”.

Dan takarar na jam'iyyar PDP, wanda ya tabbatar da cewa shi ne zai lashe zaben shugaban kasa a 2023, ya ce babbar alakarsa da kabilar Ibo za ta ci gaba da danko da kasancewa har sai sun karbi shugabancin kasar bayan wa’adin mulkinsa.

“Ina da dangantaka ta kut-da-kut da ’yan kabilar Igbo, hakan ya yi tasiri a kan zabina na Sanata Ben Obi da MPeter Obi a matsayin abokan takarata a fafatawar da na yi a baya a matsayin dan takarar shugaban kasa.
"Na sake zabar wani babban dan kabilar Ibo a nan (Dr. Ifeanyi Okowa) a karo na uku a matsayin abokin takarata.

Kara karanta wannan

Wani Sabon Hasashe Ya Tabbatar da Tinubu, Atiku Ba Za Su Lashe Zaben 2023 ba

“Ina da ‘ya’yan kabilar Igbo guda uku, kuma a karon farko ina fadin haka a bainar jama’a. Don haka dangantakata da Ndigbo ba yau ta fara ba.”

Yayin da yake alkawarin bayar da fifiko kan ayyuka a yankin Kudu maso Gabas, Atiku ya yi kakkausar suka ga gwamnatin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) kan yadda ta ware wasu sassan kasar nan da karancin ayyukan raya kasa.

“Gadar Neja ta biyu da ke Onitsha ba alheri ba ce ga yankin Kudu maso Gabas kadai, idan an yi la’akari da ita a matsayin alheri ga Najeriya ce baki daya. Domin kuwa ba mutanen Kudu maso Gabas ne kadai ke amfani da gadar ba.”

- Atiku.

Bayan Atiku Ya Kammala Wa'adin Mulkiinsa, Kudu Maso Gabas Ce Zata Samar da Shugaban Kasa, Jigon PDP

A wani labari na daban, tsohon mataimakin kakakin majalisar wakilai, Emeka Ihedioha, ya ce shugabancin Najeriya zai koma yankin Kudu maso Gabas, bayan gwamnatin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ta kammala mulki, idan ya lashe zaben 2023.

Kara karanta wannan

2023: Rawar Da Nake Takawa Na Kawo Karshen Rikicin Atiku da Wike a Sirrince, Saraki Ya Magantu

Ihedioha ya sanar da hakan ne a wani bidiyo da ya yi ta yawo a shafukan sada zumunta.

Ihedioha ya bayyana cewa 'yan Najeriya ba za su iya tafka kuskure a zaben 2023 ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel