2023: Dan Takarar Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, Ya Dira Jihar Enugu

2023: Dan Takarar Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, Ya Dira Jihar Enugu

  • Atiku Abubakar, mai neman zama shugaban kasa a 2023 ya isa birnin Enugu domin gana wa da masu ruwa da tsakin PDP
  • Gwamnan jihar Enugu, Ifeanyi Ugwuanyi, shi ne ya tarbi Atiku a Filin jirgin sama na kasa da ƙasa, tuni aka kammala shirin fara taron
  • Wannan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan gwamna Wike ya fallasa abun da ke ransa game da wasu jiga-jigan PDP

Enugu - Ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya isa jihar Enugu domin gana wa da masu ruwa da tsaki na jam'iyyar a shiyyar kudu maso gabashin Najeriya.

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku, shi ne ya bayyana haka a wani rutubu da ya saki a shafinsa na dandalin sada zumunta, Tuwita, ranar Talata 27 ga watan Satumba, 2022.

Kara karanta wannan

2023: Bayanai Sun Fito, Atiku Zai Gana Da Wasu Ƙusoshin Jam'iyyar PDP Na Kudu Maso Gabas

Atiku Abubakar a Enugu.
2023: Dan Takarar Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, Ya Dira Jihar Enugu Hoto: @Atiku
Asali: Twitter

Haka zalika, ɗan takarar ya kuma tura Hotunan lokacin da ya dira jihar, inda gwamnan jihar, Ifeanyi Ugwuanyi, ya tarbe shi hannu bibbiyu.

A sakon da ya rubuta a Tuwita, Atiku yace:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Na ji matuƙar daɗi da isowa ta jihar Enugu domin gana wa da masu ruwa da tsakin jam'iyyar PDP na baki ɗaya shiyyar kudu maso gabas."

Atiku, wanda ya isa filin tashi da saukar jiragen sama na ƙasa da ƙasa Akanu Ibiam, ana tsammanin zai wuce kai tsaye zuwa babban ɗakin taron Baze Event Centre, dake Independence Layout a birnin Enugu, inda taron zai gudana.

Me za'a tattauna a taro?

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa an shirya taron ne kan manufar, "Haɗa kan kafatanin inyamurai domin PDP," da kuma gabatar da gwamna Ifeanyi Okowa a matsayin abokin takarar Atiku.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Wutar Lantarki Ta Dauke A Najeriya Gaba Daya Da Safiyar Nan, 0 Megawatt

Tahotanni sun nuna ceqa tuni babban ɗakin taron ya cika maƙil da masoyan jam'iyyar PDP daga sassan jihohi 5 na shiyyar, suna dakon ƙarisowar Atiku.

Haka nan, an ce tuni masu ruwa da tsaki a jam'iyyar PDP da suka haɗa da mambobin majalisar zartarwar jam'iyya ta jiha, yan majalisu da sauransu, suka nemi wuri suka zauna a ɗakin taron.

A wani labarin kuma Atiku Ya Naɗa Saraki, Shekarau da Wasu Jiga-Jigan PDP a Wasu Manyan Muƙaman Kamfe

Mai neman zama shugaban ƙasa a inuwar PDP, Atiku Abubakar, ya sake yin wasu muhimman naɗe-naɗe a tawagarsa.

Tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, da Sanata Ibrahim Shekarau sun samu shiga sabon naɗin Atiku.

Asali: Legit.ng

Online view pixel