'Yan Bindiga Sun Kashe Jami'in Ɗan Sanda Mai Mukami, Sun Sace Matafiya a Katsina

'Yan Bindiga Sun Kashe Jami'in Ɗan Sanda Mai Mukami, Sun Sace Matafiya a Katsina

  • Wasu tsagerun 'yan bindiga sun harbe Insufektan 'yan sanda har lahira a kan titin Katsina zuwa Jibiya
  • Rahoto ya nuna cewa mamacin ya yi kokarin daƙile harin yan ta'addan ne amma ya gamu da ajalinsa, sun yi awon gaba da matafiya
  • Kakakin hukumar 'yan sanda reshen jihar Katsina, SP Gambo Isah, yace nan ba da jima wa ba zai yi hira da 'yan jarida

Katsina - Wasu rahotanni sun nuna cewa wani ɗan sanda mai muƙamin Insufekta, Idris Musa ya rasa rayuwarsa yayin fafata wa da yan bindiga a Makera Quaters, ƙauyen Kwakware dake Titin Katsina-Jibiya.

Wani ganau da ba'a faɗi sunansa ba ya shaida wa Channels tv cewa yan ta'addan sun shiga ƙauyen ranar Litinin da misalin ƙarfe 7:00 suna harbi kan mai uwa da wabi yayin da suka biyo wata Motar Bas.

Harin 'yan bindiga a Katsina.
'Yan Bindiga Sun Kashe Jami'in Ɗan Sanda Mai Mukami, Sun Sace Matafiya a Katsina Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

A cewar wata majiya, yunƙurin marigayi Insufekta na daƙile harin tawagar 'yan ta'addan bai kai ga nasara ba, yayin da suka yi musayar wuta, hakan ya yi sanadin mutuwarsa.

Bayan sun harbe shi har lahira, an ce 'yan ta'addan sun kuma ƙona motarsa, daga bisani kuma suka yi awon gaba da Fasinjoji masu yawa zuwa maɓoyarsu da ba'a sani ba, kamar yadda Guardian ta ruwaito.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ko Hukumomi sun ɗauki mataki?

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa har zuwa yanzun da muke haɗa wannan rahoton hukumar yan sanda ba tace komai ba game da mutuwar jami'inta da kai harin.

Haka zalika da aka tuntuɓi mai magana da yawun hukumar yan sanda ta jihar Katsina, SP Gambo Isah, yace yana cikin taro ne a lokacin amma zai yi jawabi ga 'yan jarida nan da awa ɗaya.

A wani labarin kuma 'Yan Bindiga Sun Kai Sabon Kazamin Hari Kan Bayin Allah, Sun Kashe Rayuka a jihar Zamfara

Aƙalla mutum uku suka rasa rayukansu kuma aka sace mata masu shayarwa Takwas yayin da wasu yan bindiga suka kai hari yankin Tauji, Kanoma ta arewa, ƙaramar hukumar Maru a jihar Zamfara.

Wani ɗan asalin yankin, Muhammad Maisa, wanda ya zanta da jaridar Punch, yace lamarin ya faru da misalin ƙarfe 1:40 na dare lokacin da wasu sanannun 'yan bindiga suka shigo yankin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel