Jerin Kasuwanci 6 da Zasu Amfana da Yaƙin Neman Zaben Shugaban Kasa 2023

Jerin Kasuwanci 6 da Zasu Amfana da Yaƙin Neman Zaben Shugaban Kasa 2023

A yau Laraba, 28 ga watan Satumba, 2022 jam'iyyu zasu kaɗa gangar yaƙin neman zaɓe domin tunkarar babban zaɓen 2023 kamar yadda hukumar INEC ta tsara a jadawalinta.

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa jam'iyyu 18 ne suka tsayar da 'yan takarar shugbaan ƙasa, waɗanda ke hanƙoron kujerar da shugaba Buhari ke zaune.

Daga cikin masu neman kujera lamba ɗaya a Najeriya akwai, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu na jam'iyyar APC, Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP, Rabiu Kwankwaso na jam'iyyar NNPP da kuma Peter Obi na Labour Party.

Buhari a lokacin kamfe.
Jerin Kasuwanci 6 da Zasu Amfana da Yaƙin Neman Zaben Shugaban Kasa 2023 Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Najeriya zata shaida manyan harkokin kamfe waɗanda ka iya taɓa tattalin arzikin kasa. A zaɓen da ya wuce 2019 an ƙayyade iyakar kudin da kowace jam'iyya zata iya kashe wa Biliyan ɗaya.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Babbar Kotu Ta Soke Takarar Sanata Adamu Alieru a Jihar Kebbi

Amma a zaɓen 2023, masu dokoki sun sake nazari sun ɗaga kuɗin zuwa biliyan N5bn a kundin zaɓe 2022.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A wani rahoton Cibiyar nazarin tattalin arziki ta nahiyar Afirka, kokarin jawo hankalin mutane da nufin tattara kuri'unsu lokacin kamfe shi ke ingiza gwamnati da 'yan siyasa kashe maƙudan kudi watanni gabanin zaɓe.

A lokaci irin wannan, akwai yuwuwar hada-hadar kuɗaɗe kan dalilai daban-daban. Alal misali lokacin zaɓen fidda gwanin manyan jam'iyyu, APC da PDP, ana ganin sun taka rawa wajen ƙarancin dalar Amurka a ƙasa.

Legit.ng Hausa ta bincika tare da nazari kan wasu ɓangarorin tattalin arziki da kasuwarsu zata ɗaga yayin harkokin kamfe da za'a soma yau.

Kasuwancin Sufuri zai buƙasa

Mafi yawan 'yan takara, musamman masu neman zama shugaban kasa da makusantansu zasu karaɗe jihohi domin yaɗa manufarsu. Hakan zai jawo liyafar ɓangaren Sufuri ta ɗaga, wanda ya haɗa ɗa Jiragen sama da motocin Bas.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: 'Yan Bindiga Sun Bude Wa Ɗan Takarar NNPP Wuta a Jihar Arewa

Masu Hoto da Zane-Zane

Banoni, fastoci da ƙananan rigunan da ake gyara wa da sauran makamantansu na daga cikin kayayyakin da masu neman takara ke amfani da su domin ɗaga darajarsu lokacin kamfe.

Bisa la'akari da haka kasuwancin masu tsara Hotuna zai ɗaga a faɗin sassan ƙasar nan domin za'a nemi su yi ayyuka.

Masu tsara wurin taro

Yan takara zasu fifita ayyukan masu ƙayata wurin taro waɗanda zasu tsara tare da kula da kayayyakin da za'a yi amfani da su a tarukan Kamfe.

Za'a samu tsananin neman ɗakunan taro, runfuna, Kayan sauti, masu tsara cikin ɗakin taro da sauransu. Mutanen dake ɓangaren masana'antun waɗan nan kayayyaki zasu amfana.

Masu ba da Nishadi

Ba za'a bar ɓangaren nishaɗi a baya ba daga cikin waɗanda zasu amfani da lokacin kamfen 2023. A shekaru da dama, ana jawo fitattu a ɓangaren kai tsaye cikin siyasa ko ta hanyar da suka ƙware.

Kara karanta wannan

Jonathan Ya Fallasa Wasu Yan Takara, Ya Gargaɗi 'Yan Najeriya Kada Su Zaɓe Su a 2023

Ana biyan mawaƙa su rera waƙa a wurin Kamfe domin nishaɗantar da dandazon mutane da kuma zuzuta nagartar yan takara.

A arewacin Najeriya, fitattu a wannan bangaren sun haɗa da Dauda Rarara da Naziru Ahmad, waɗanda ake biya su yi amfani da basirarsu da kalaman dusashe tsagin hamayya da gwarzanta yan takara.

Haka zalika mawaƙa kamar Alhaji Wasi'u Ayinde, da David Adeleke, wanda aka fi sani da Davido na daga cikin waɗanda tauraruwarsu ke haskawa lokacin Kamfe.

Masu gidan abinci da Otal zasu shana

Yayin da 'yan siyasa da magoya bayansu zasu karaɗe sassan ƙasar nan, za'a bukaci abinci da kuma wurin kwana. Ɓangaren masu shirya liyafa zasu ga cigaba a kasuwancinsu.

Kafafen watsa labarai

Sanya tallace-tallace a kafafen watsa labarai da gida na na ƙasa da ƙasa, hira a Talabijin da sauransu zasu ci kasuwa sosai yayin da harkokin siyasa ya kankama a 'yan watanni masu zuwa.

A wani labarin kuma kun ji cewa Gwamnan PDP Ya Yi Watsi da Atiku Yayin da Ya Kai Ziyara Kudu Maso Gabas

Kara karanta wannan

Rikicin PDP Na Tura Mummunan Sako Ga Yan Najeriya Game da Zaɓen 2023, Wike

Gwamnan jihar Abiya, Okezie Ikpeazu, ya yi watsi da zuwan Atiku yankin kudu maso gabas, bai halarci wurin taron ba.

Mai neman shugaban kasa a PDP, Atiku Abubakar, ya kai ziyara Enugu domin gana wa da masu ruwa da tsakin jam'iyya na yankin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel