Gwamnan Arewa Ya Bayyana Wadanda Za Su Tafiyar Da Gwamnatin Tinubu Idan Aka Zabe Shi

Gwamnan Arewa Ya Bayyana Wadanda Za Su Tafiyar Da Gwamnatin Tinubu Idan Aka Zabe Shi

  • Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya bayyana cewa gwamnatin dan takarar shugaban kasa na APC, Bola Tinubu za ta cika da matasa idan aka zabe shi
  • Gwamnan ya bayyana cewa Tinubu zai zabo kwararru da gogaggu ne kawai, amma matasa ne za su tafiyar da harkokin gwamnatin
  • A kwanan nan ne aka nada gwamnan na Kogi a matsayin jagoran matasa na kungiyar kamfen din Tinubu-Shettima

Kogi - Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya bayyana cewa matasa ne za su tafiyar da gwamnatin Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) idan aka zabe shi.

Bello na daya daga cikin sabbin mambobin kungiyar kamfen din Tinubu-Shettima inda aka nada shi a matsayin jagoran matasanta na kasa, Vanguard ta rahoto.

Tinubu da Bello
Gwamnan Arewa Ya Bayyana Wadanda Za Su Tafiyar Da Gwamnatin Tinubu Idan Aka Zabe Shi Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Alhaji Yahaya Bello
Asali: Facebook

Yayin da yake sanar da nadin nasa, Tinubu ya bayyana nasarorin siyasa da irin shugabanci abun koyi da gwamnan ya nuna a jiharsa da kuma a matsayinsa na dan jam’iyya.

Kara karanta wannan

Inyamuri ba zai gaji Buhari ba, gwamnan yankin Kudu ya bayyana dalilai

Tinubu zai samar da kwararru da gogaggu ne kawai idan aka zabe sa - Bello

A wata hira da Channels TV a ranar Litinin, gwamnan na Kogi ya bayyana Tinubu a matsayin shugaba da zai saurari matasan Najeriya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Da izinin Allah, matasan Najeriya za su tantance da gudanar da harkoki da gwamnatin Sanata Bola Ahmed Tinubu idan aka rantsar da shi.
“Zai samar da abun bukata, zai samar da kwararru, zai samar da gogewar ya dukkanin matasan Najeriya don cimma cikakkiyar damarmu."

Gwamnan Arewa Ya Mance Da Batun Tinubu, Ya Fadi Wanda Zai Sa Ya Gaji Buhari Da Yana Da Iko

A wani labarin, gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello, ya bayyana cewa da ace yana da ikon zartar da hukunci da babu makawa takwaransa na jihar Ekiti, Kayode Fayemi zai nada a matsayin shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Zabi Gwamnan APC, Ya Bi Shi Babban Aiki a Yakin Zama Shugaban Kasa

Sani Bello ya bayyana Fayemi wanda ya nemi tikitin takarar shugaban kasa na APC, a matsayin aminin jiharsa tunma kafin ya zo neman kuri’u a kudirinsa na son zama shugaban kasa.

Gwamnan na Neja ya bayyana hakan ne yayin da ya tarbi Fayemi a gidan gwamnati da ke garin Minna, babbar birnin jihar a yammacin ranar Lahadi, Leadership ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel