Tinubu Ya Zabi Gwamnan APC, Ya Bi Shi Babban Aiki a Yakin Zama Shugaban Kasa

Tinubu Ya Zabi Gwamnan APC, Ya Bi Shi Babban Aiki a Yakin Zama Shugaban Kasa

  • Rotimi Akeredolu shi ne wanda zai jagoranci yakin neman zaben jam’iyyar APC a Kudu maso yamma
  • Gwamnan jihar Ondo ya bada sanarwar cewa an nada shi wannan aiki ne ta hannun Richard Olatunde
  • Jawabin sakataren yada labaran Gwamnan yace an zabe shi ne saboda irin kokarinsa da kwarewarsa

Abuja - Gwamna Rotimi Akeredolu na jihar Ondo ya zama jagoran yakin neman zaben Tinubu-Shettima na kudu maso gabashin Najeriya.

The Nation ta fitar da rahoto cewa Asiwaju Bola Tinubu ya amince Mai girma Rotimi Akeredolu ya jagoranci takararsa a yankin Kudu maso yamma.

Sakataren yada labaran gwamnan, Richard Olatunde ya fitar da jawabi na musamman a ranar Litinin dinnan, ya tabbatar da nadin mukamin.

Kamar yadda jawabin Richard Olatunde ya nuna, tun 8 ga watan Agustan 2022, aka aikowa Akeredolu takardar sanar da shi ba shi wannan aiki.

Kara karanta wannan

Zulum da Gwamnonin Jihohin Arewa Maso Gabas Sun Jerowa Buhari Bukatunsu

Hadimin gwamnan yace an zabi Mista Akeredolu ne saboda gogewarsa a siyasa da kuma jagorancin da ya nuna a matsayin 'dan jam'iyyar APC.

Bugu da kari, Akeredolu SAN shi ne shugaban gwamnonin kudu maso yammacin Najeriya, yana cikin masu adawa mulki ya cigaba da zama Arewa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rotimi Akeredolu
Rotimi Akeredolu da Bola Tinubu Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC

Jawabin Richard Olatunde

“Da wannan takarda, muna farin cikin nada ka a matsayin shugaban kamfe na kwamitin takarar shugaban kasar Tinubu/Shettima (a Kudu maso yamma).
Wannan mukami ya dace kuma ya cancanta, inda aka yi duba da nasarorin da ka samu a siyasa, da irin jagorancin da ka nuna a kujerar gwamna da jam’iyya.”

- Richard Olatunde

Daily Post tace an yi kira Gwamnan na jihar Ondo ya dage wajen kai APC ga ci a 2023.

"Muna farin ciki da ka shigo kwamitin kamfe din mu. Mun san za kayi akin kokarinka wajen sauke wannan sabon nauyi da aka daura maka yayin da muka shiga neman takaran da zai kai mu ga asara a zaben shugaban kasa na 2023."

Kara karanta wannan

Baya da kura: Atiku Ya Sheka Kasar Waje, Maganar Shawo Kan Rikicin PDP Ya Wargaje

- Richard Olatunde

Bola Tinubu yana takara APC, zai gwabza da Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP, Peter Obi a jam’iyyar LP da ‘dan takarar NNPP, Rabiu Kwankwaso.

APC za ta ci zabe a 2023

Dazu kun ji labari Laftanan Janar Tukur Yusuf Buratai mai ritaya da Air Marshal Abubakar Sadique mai ritaya sun zaburar da matasan APC.

Tsofaffin hafsoshin sojojin na kasar nan sun yi kira ga matasa su jawo mutanen Najeriya duk su zabi All Progressives Congress (APC) a 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel