Gwamnan Arewa Ya Mance Da Batun Tinubu, Ya Fadi Wanda Zai Sa Ya Gaji Buhari Da Yana Da Iko

Gwamnan Arewa Ya Mance Da Batun Tinubu, Ya Fadi Wanda Zai Sa Ya Gaji Buhari Da Yana Da Iko

  • Gwamna Abubakar Sani Bello ya bayyana wanda zai tsayar a matsayin magajin Shugaba Buhari idan da ace yana da iko
  • Bello ya ce babu makawa gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi, zai nada a matsayin shugaban kasa a 2023 da ace shine ke zabar shugaba
  • Ya bayyana cewa hankalinsa zai kwanta idan takwaran nasa ya zama shugaban kasa don zai dunga ganinsa kai tsaye ba tare da shamaki ba

Niger - Gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello, ya bayyana cewa da ace yana da ikon zartar da hukunci da babu makawa takwaransa na jihar Ekiti, Kayode Fayemi zai nada a matsayin shugaban kasa.

Sani Bello ya bayyana Fayemi wanda ya nemi tikitin takarar shugaban kasa na APC, a matsayin aminin jiharsa tunma kafin ya zo neman kuri’u a kudirinsa na son zama shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Samu Gagarumin Goyon Baya Daga Wani Shahararren Malamin Addini, Ya Ce Shine Zai Gyara Najeriya

Fayemi da Bello
Da Ina Da Iko Fayemi Zan Ba Takara A APC ba Tinubu Ba, Gwamnan Arewa Hoto: Fayemi da Bello
Asali: UGC

Gwamnan na Neja ya bayyana hakan ne yayin da ya tarbi Fayemi a gidan gwamnati da ke garin Minna, babbar birnin jihar a yammacin ranar Lahadi, Leadership ta rahoto.

Wata sanarwa da kakakin kungiyar yakin neman zaben Fayemi, Femi Ige ya saki a ranar Litinin, ya nakalto gwamnan na jihar Neja yana cewa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Ka zo nan akalla sau uku ko hudu kafin yanzu. Ka kasance amini ga jihar Neja. Ba wai a yanzu da bukatar neman goyon baya ya taso da mutane ke zuwa ba.
“Mutum biyar ko shida ne kawai suka zo jihar amma kana da cikakken goyon bayana. Idan ka zama shugaban kasa, zan huta saboda na san zan ganka cikin sauki. A zahirin gaskiya, da ace ina da dama zan nada ka a matsayin shugaban kasa na gaba bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari.”

Kara karanta wannan

Rashin Lafiya: "Ba Kan Tinubu Farau Ba Kowa Da Matsalar Shi", Jigon APC Ya Yi Martani Mai Zafi

Ige ya kuma nakalto cewa gwamna Bello ya ce koda dai bai taba shiga tarurruka ko zabuka ba, dan takarar ya cancanta kuma yana da tabbacin cewa wakilan jihar Neja sun goyi bayansa.

Tinubu Ya Samu Gagarumin Goyon Baya Daga Wani Shahararren Malamin Addini, Ya Ce Shine Zai Gyara Najeriya

A wani labarin, shugaban kungiyar Young Professionals of Nigeria (YPN), Fasto John Desmond, ya nuna goyon bayansa ga dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

Desmond ya yi kira ga yan Najeriya da su zabi Tinubu a matsayin shugaban kasa a babban zaben 2023 mai zuwa.

Ya yi kiran ne Umuahia, jihar Abia, yayin wani rangadi na wayar da kan matasan kungiyar YPN wadanda suke mambobin APC a fadin kudu maso gabas, jaridar The Nation ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel