Gwamna Wike Na PDP Ya Gana da Tsohon Dan Takarar Shugaban Kasan APC, Yahaya Bello

Gwamna Wike Na PDP Ya Gana da Tsohon Dan Takarar Shugaban Kasan APC, Yahaya Bello

  • Yadda gwamnan PDP Nyesom Wike bibiyar jiga-jigan jam'iyyar APC abu ne da ke kada hantar 'yan PDP a fadin Najeriya
  • A yau Juma'a ne aka ga gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello tare da gwamnan jiharsa ta Ribas yayin da ya ziyarce shi
  • Joe Igbokwe ya bayyana imaninsa da cewa, gwamna Wike na ci gaba da rabar APC ne don yiwuwar shiga cikinta

Jihar Ribas - Yayin da yake ci gaba da rikici da dan takarar shugaban kasan PDP, gwamna Wike na ci gaba da kada hantar Atiku ta hanyar tarbar 'yan jam'iyyar adawa a jiharsa.

A wasu hotunan da Joe Igbokwe ta yada a Facebook ranar Juma'a 16 ga watan Satumba, an sake ganin gwamna Wike da jigon jam'iyyar APC, Alhaji Yahaya Bello.

Gwamna Wike ya gana da Yahaya Bello a Ribas
Gwamna Wike Na PDP Ya Gana da Tsohon Dan Takarar Shugaban Kasan APC, Yahaya Bello | Hoto: Joe Igbokwe
Asali: Facebook

A wannan karon, gwamna Wike ya karbi bakuncin gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a jiharsa ta Ribas.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar PDP Ba Ta Dan Takaran Gwamna a Zaben 2023, Kotu Ta Soke Zaben Fidda Gwani

Har ya zuwa yanzu dai ba a san me suka tattauna ba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Joe ya rubuta cewa:

"Mutumin na Tinubu, gwamna Yahaya Bello tare da gwamna Wike a jihar Ribas a yau. Lissafin na kara rubanya kansa."

Shin Wike zai koma APC?

Sai dai, gwamna Wike ya ce sam ba zai shiga APC ba, kuma ba zai yiw aikin don tallata dan takararta Tinubu ba a zaben 2023 mai zuwa.

Hakazalika, wani na kusa da shi bayyana cewa, Wike ba zai goyi bayan Atiku Abubakar ba, kuma bai da alaka da APC kasancewar ta zabo musulmi a matsayin abokin takara.

Manyan jam'iyyun siyasan biyu (APC da PDP) na ci gaba da fuskantar kalubalen rikicin cikin gida tun bayan kammala zaben fiida gwani.

Ku Yi Watsi da Tinubu, Atiku da Obi, Shawarin Kwankwaso Ga ’Yan Najeriya

Kara karanta wannan

Matashi Ya Fasa Auren Budurwa Saboda Ta Ki Bayyana Wanda Ya Bata Kyautan IPhone13 ProMax

A wani labarin, dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso ya ba 'yan Najeriya shawari kyauta, ya su kiyayi kansu su yi watsi da 'yan takarar shugaban kasa a APC, PDP da LP.

Ya yi kira ga 'yan Najeriya da kada su zabi Bola Ahmad Tinubu, Atiku Abubakar ko Peter Obi a zaben 2023 mai zuwa, Premium Times ta ruwaito.

A fahimtar Kwankwaso, ya kamata 'yan Najeriya su nisance 'yan takarar saboda basu da wani abin a zo a gani da za su iya ba kasar bayan an zabe su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel