Jam'iyyar PDP Ba Ta Dan Takaran Gwamna a Zaben 2023, Kotu Ta Soke Zaben Fidda Gwani

Jam'iyyar PDP Ba Ta Dan Takaran Gwamna a Zaben 2023, Kotu Ta Soke Zaben Fidda Gwani

  • Kotu ta fitittiki dan takarar kujerar gwamna na jam'iyyar PDP a jihar Zamfara, Hon Dauda Lawal
  • Kotun tarayya ta baiwa hukumar INEC umurnin ta gaggauta shirya sabon zaben fidda gwani
  • Lauyoyin Dauda Lawal sun bayyana cewa zasu daukaka kara a kotun Afil

Wata babbar kotun tarayya dake Gusau, jihar Zamfara, ta soke zaben Dauda Lawal a matsayin dan takaran gwamnan jihar na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

Lawal ya lashe zaben fidda gwanin jam'iyyar ne a ranar 25 ga watan Mayu, 2022.

Wasu yan takarar uku, — Abubakar Nakwada, Wadatau Madawaki, and Ibrahim Shehu-Gusau — sun janye daga zaben saboda zargin magudi.

Amma Adamu Maina, baturen zaben yayi watsi da janyewarsu saboda basu janye a hukumance ba.

Amma a watan Yuni, wasu yan takara hudu suka shigar da kara kotu inda suka bukaci kotu tayi watsi da zaben.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: 'Yan Arewa sun fi karbar Tinubu fiye da Atiku da Kwankwaso, inji jigon APC

A ranar Juma'a 16 ga Satumba, Alkali Aminu Bappa, ya yanke hukuncin watsi da zaben.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya bada umurnin gudanar da sabon zaben fidda gwani idan PDP na son musharaka a zaben 2023.

PDP Pa
Jam'iyyar PDP Ba Ta Dan Takaran Gwamna a Zaben 2023, Kotu Ta Soke Zaben Fidda Gwani

Lauyan wadanda suka shigar da kara, Ibrahim Aliyu, ya bayyana farin cikinsa bisa wannan nasara da suka samu.

A cewarsa:

"Muna farin ciki kotu ta amsa bukatunmu kuma ta soke zaben da ke cike da magudi."

Amma mai magana da dan takaran gwamnan, Imraan Ahmad, yace maigidansa zai daukaka kara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel