Matashi Ya Fasa Auren Budurwa Saboda Ta Ki Bayyana Wanda Ya Bata Kyautan IPhone13 ProMax

Matashi Ya Fasa Auren Budurwa Saboda Ta Ki Bayyana Wanda Ya Bata Kyautan IPhone13 ProMax

  • Wani matashin ya soke auren da aka sa rana da budurwarsa kan zargin tana alaka da wasu mazaje
  • Budurwar ta koma gida da sabon wayar iPhone 13 Pro Max kuma tayi ikirarin wani dan'uwanta ya saya mata
  • Saurayin ya tambayeta ta bayyana sunan dan'uwan da ya bata wayar amma taki

Wani matashi ya fasa auren budurwarsa bayan sabanin da suka samu kan lamarin sabuwar wayar zamani iPhone 13 Pro Max.

Yayinda ake shirye-shiryen aure bayan sa musu rana, dare daya budurwar ta kawo wayar mai kimanin kudi N800,000 gida.

Iphone 13
Matashi Ya Fasa Auren Budurwa Saboda Ta Ki Bayyana Wanda Ya Bata Kyautan IPhone13 ProMax Hoto: @Rita_Amy
Asali: Instagram

Ganinta da wayar ke da wuya, sai saurayin ya tambayeta shin ina ta samu waya mai tsada haka, sai tace wani dan'uwanta ne ya bata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Ni Fa Don Kudi Zan Yi Auren Nan: Budurwa Mai Shirin Aure Ta Bayyana

Yayinda ya bukaci sanin sunan 'danuwan saboda ya tabbatar da gaskiyar lamari, budurwar taki kuma hakan ya bata masa rai.

Hakan yayi sanadiyar soke auren, kamar yadda @Rita_Amy ta bayyana a kafar sada ra'ayi da zumunta na TikTok.

A bidiyon da ta saki, tace saurayin abokinta ne.

Kalli bidiyon:

Asali: Legit.ng

Online view pixel