Rikicin Cikin Gidan PDP Ya Fito Baro-baro, Gwamnoni 8 Sun Ki Zuwa Taron Jam’iyya

Rikicin Cikin Gidan PDP Ya Fito Baro-baro, Gwamnoni 8 Sun Ki Zuwa Taron Jam’iyya

  • Gwamnonin PDP takwas aka samu labari sun ki zuwa wajen taron da shugabannin jam’iyya suka yi
  • A tsakiyar makon nan ne jam’iyyar PDP tayi wani muhimmin taro domin dinke baraka da fara shirin 2023
  • Nyesom Wike da wasu Gwamnoni da ke tare da shi a rikicinsa da Atiku Abubakar sun ki zuwa wajen taron

Abuja - Akalla gwamnonin jihohi takwas ne ba a gani ba a wajen wani taro na jam’iyyar PDP da aka shirya a ranar Laraba, 7 ga watan Satumba 2022.

Labarin da muka samu daga gidan talabijin na AIT shi ne shugabannin jam’iyyar hamayyar sun yi zama ne a Abuja, inda aka tattauna batutuwan zabe.

Taron ya samu halartar shugaban jam’iyya na kasa, Iyorchia Ayu da shugaban majalisar amintattu, Walid Jibrin, wanda ake zargin kujerunsu na rawa.

Kara karanta wannan

2023: Motocin Yakin Neman Zaben PDP Na Wata Jiha Sun Ta Da Kura, Babu Hoton Atiku Abubakar

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Arch. Muhammad Namadi Sambo da Atiku Abubakar sun je wajen taron, amma ba a ga keyar wasu gwamnoni ba.

Baraka ta dinke a PDP?

Rahoton yace an shirya taron ne da nufin magance rigimar cikin gidan da ta bijiro bayan tsaida ‘dan takara, sai dai da alama, ba a kai ga yin sulhu ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Nyesom Wike da gwamnonin jihohin PDP da ke tare da shi wajen rigima da bangaren Atiku Abubakar, sun yi amfani da taron wajen fito da fushin na su.

PM News wanda ta fitar da wanan rahoto a jiya, ba ta iya kawo jerin sunayen gwamnonin jam’iyyar hamayyar da suka kauracewa wannan zaman ba.

Sai dai muna da labari cewa daga cikin gwamnonin da ke gaba-gaba a bangaren Wike akwai Gwamna Seyi Makinde (Oyo) da Samuel Ortom (Benuwai).

Kara karanta wannan

2023: Gangamin Taron Kamfen PDP a Edo Ya Sake Fito da Rikicin Jam'iyyar, Atiku Ya Shiga Matsala

Sauran gwamnonin jihohi masu-ci da ake tunani ba su tare da ‘dan takarar shugaban kasar sun hada da Ifeanyi Ugwuanyi (Enugu) da Okezie Ikpeazu (Abia)

Aminu Waziri Tambuwal shi ne shugaban kungiyar gwamnonin jihohin da PDP ta ke mulki. Gwamnan na Sokoto yana cikin na gaban goshin ‘dan takaran.

Bayan taron, Sakataren yada labaran PDP na kasa, Debo Ologunagba yace har aka tashi wannan zama, ba ayi maganar shugaban PDP ya yi murabus ba.

Atiku ya zauna da 'yan takara

Ku na sane da cewa Atiku Abubakar yayi takara da su Nyesom Wike, Bukola Saraki, Anyim Pius Anyim da Bala Mohammed a zaben fitar da gwani na 2023.

Mun ji labari akwai wadanda suka shiga zaben ‘dan takara na PDP da sun ki yarda su gana da Atiku Abubakar wanda zai rike tuta jam’iyya a shekara mai zuwa.

Kara karanta wannan

Kwamitin Takara: Fasto ya Kunyata APC, Yace Ba Zai Yi Wa Tinubu Kamfe a 2023 ba

Asali: Legit.ng

Online view pixel