An Girke Jami’an Tsaro Carko-Carko a Sakateriyar APC, Tinubu da Shettima Za Su Kai Ziyara

An Girke Jami’an Tsaro Carko-Carko a Sakateriyar APC, Tinubu da Shettima Za Su Kai Ziyara

  • An girke jami'an tsaro a sakateriyar APC yayin da ake sa ran Tinubu da Shettima za su kai ziyara
  • Tinubu da Shettima za su kai ziyarar ne ta farko tun bayan kammala zaben fidda gwani na jam'iyyar
  • A ranar 28 ga watan nan ne za a fara gangamin kamfen din 'yan takarar shugaban kasa, kowacce jam'iyya na shiri

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

FCT, Abuja - Dan takarar shugaban kasa Asiwaju Bola Tinubu da mataimakinsa Sanata Kashim Shettima za su kai ziyara sakateriyar jam'iyyar APC a yau Laraba, 7 ga watan Satumba, Punch ta ruwaito.

Rahoton da muke samu ya ce, tuni an girke jami'an tsaro ta kowacce kofa da sakon sakateriyar a shirye-shiryen karbar jiga-jigan na APC.

An ga motocin sintiri da dama a zagaye da sakateriyar manyan jami’ai dake kai komo a zagayenta.

Kara karanta wannan

2023: Atiku ya gana da wasu tsoffin shugabannin siyasar kasar nan, sun yi wata tattaunawa

Tinubu da Shettima za su kai ziyara sakateriyar APC
An Girke Jami’an Tsaro Carko-Carko a Sakateriyar APC, Tinubu da Shettima Za Su Kai Ziyara | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

An ce Tinubu da Shettima za su halarci wata ganawar wucin gadi ne da kwamitin ayyuka na jam’iyyar APC na kasa a sakatariyar da misalin karfe 10:00 na safe.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na zuwa ne bayan watanni uku da Tinubu ya dage kai ziyarar farko ga sakatariyar bayan lashe zaben fidda gwanin shugaban kasa da aka a APC.

Duk da cewa babu wata sanarwa a hukumance daga jam’iyyar APC, majiya ta ce ganawar za ta ba da damar tattaunawa kan shirin kamfen din Tinubu da kuma sake fasalin tsarin shi kansa kamfen din da za a fara a ranar 28 ga watan nan.

Hakazalika, majiyar ta kuma kara da cewam za a takaita adadin wadanda za su shiga cikin sakatariyar domin rage cunkoson jama’a da kuma wasu dalilai na tsaro.

Ana sa ran Tinubu da Shettima su yiwa manema labarai bayani a sakateriyar jam’iyyar ta APC bayan kammala ganawar.

Kara karanta wannan

Jami'ar Arewa ta yi watsi da ASUU, ta ce malamai su gaggauta dawowa bakin aiki

Jerin 'Yan Siyasan Najeriya da Kungiyoyin Dake Yiwa Tinubu Gangamin 2023

A wani labarin, babu shakka, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ko kwararre ne wajen kitsa tafiyar siyasa tare da zabo wadanda suka cancanta a tafiyarsa.

Ya zuwa yanzu dai Tinubu ya yi cudanya da jiga-jigan siyasa a ciki da wajen Najeriya yayin da yake ci gaba da tallata aniyarsa ta neman gaje shugaban kasa Muhammadu Buhari a 2023.

A yankin Kudu maso Yammacin Najeriya, tsohon gwamnan na Legas sananne ne wajen kitsawa da daura wasu fitattun 'yan siyasa a kujeru daban-daban, musamman gwamnoni.

Asali: Legit.ng

Online view pixel