Bayan Kiran Dalibai, Jami’ar Gombe Ta Yi Watsi da ASUU, Ta Kira Malamai Su Dawo Aiki

Bayan Kiran Dalibai, Jami’ar Gombe Ta Yi Watsi da ASUU, Ta Kira Malamai Su Dawo Aiki

  • Jami'ar jihar Gombe ta yi kira ga malamanta dake karatu a fadin Najeriya da su gaggauta dawowa aiki
  • Jami'ar ta rantsar da daliban ajin farko na zangon wannan shekara, duk da kuwa ana ci gaba da yajin ASUU
  • Jami'o'in Najeriya sun shafe sama da kwanaki 200, lamarin dake kara dagula lamurran ilimi a Najeriya

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jihar Gombe - Hukumar gudanarwar jami'ar jihar Gombe (GSU) ta kira dukkan malaman ta bukaci dukkam ma'aikatanta dake hutun karatu da su gaggauta dawowa aiki.

Wannan na zuwa kira na zuwa ne a yau Litinin 5 ga watan Satumba, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Magatakardar jami’ar, Dakta Abubakar Aliyu Bafeto, a cikin wata takarda mai dauke da kwanan watan Satumba 5, 2022, ya umurci malaman jami'ar da ke karatu a Najeriya da su koma bakin aiki kasancewar jami'ar ta dawo karatu.

Jami'ar Gombe ta janye daga ASUU, ta nemi malamai su dawo bakin aiki
Bayan Kiran Dalibai, Jami’ar Gombe Ta Yi Watsi da ASUU, Ta Kira Malamai Su Dawo Aiki | Hoto: hotels.ng
Asali: UGC

Idan baku manta ba, jami'o'in Najeriya na rufe tun watan Fabrairun bana, inda aka shafe kwanaki sama da 200 ana cikin yajin aiki.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A baya kadan, jami'ar ta umarci dalibai da su dawo karatu a cikin watan nan na Satumba, lamarin da ya tunzura kungiyar malaman jami'a ta ASUU.

A ranar Asabar din da ta gabata ne jami'ar ta rantsar da sabbin dalibai 'yan ajin farko tare da bayyana shirin komawa karatu gadan-dagan.

Sai dai shugaban kungiyar GSU reshen ASUU, Dakta Suleiman Salihu Jauro, ya ce kungiyar bata amince da umarnin da mahukuntan jami’ar suka bayar na komawa bakin aiki ba.

Sai abin da ASUU tace, inji wani malami

Wani malamin da a tsangayar lissafi da kwamfuta da ya nemi a sakaya sunansa ya ce, ya gaza fahimtar lamarin, domin ya fahimci ASUU da hukumomin jami'ar basu fahimci juna ba.

Ya shaidawa wakilin Legit.ng Hausa a jihar Gombe cewa:

"Ko yau din nan ASUU reshen GSU ta fitar sanarwa cewa yaji ba gudu ba ja da baya, don haka bansan me zan ce maka ba.
"Idan ka duba maganan GSU da ASUU, akwai alamar ba su fahimci juna ba. Duk da haka inaga abinda zan ce maka shine, muna jiran meye ASUU za su ce, sannan meye makomar aikinmu.
"Gwamnatin jiha mukewa aiki, su suka tura mu karin karatu, amma ASUU kungiyar mu ce da ke kula da jin dadi da mutuncin ma'aikata. To ni dai abinda zan ce sai na ji batun ASUU kuma akwai iri na da yawa."

Jami'ar Gombe ta yi watsi da yajin ASUU, ta nemi dalibai su dawo karatu

A wani labarin, jami'ar jihar Gombe (GSU) ta yi kira ga daliban aji daya da su gaggauta dawowa makaranta domin kammala rajista, kana su kare karatun zangon farko na 2021/2022 da aka fara.

Jami'ar ta fara rajistar daliban aji daya kafin fara yajin aikin ASUU a watan Fabrairu, lamarin da ya kawo tsaiko ga rajistar da ci gaba da karatun zangon.

A wata sanarwa da aka aikowa wakilin Legit.ng Hausa, jami'ar ta ce ta yi shawari, ta kuma amince daliban su dawo domin ci gaba da karatu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel