Jerin 'Yan Siyasan Najeriya da Kungiyoyin Dake Yiwa Tinubu Gangamin 2023

Jerin 'Yan Siyasan Najeriya da Kungiyoyin Dake Yiwa Tinubu Gangamin 2023

Babu shakka, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ko kwararre ne wajen kitsa tafiyar siyasa tare da zabo wadanda suka cancanta a tafiyarsa.

Ya zuwa yanzu dai Tinubu ya yi cudanya da jiga-jigan siyasa a ciki da wajen Najeriya yayin da yake ci gaba da tallata aniyarsa ta neman gaje shugaban kasa Muhammadu Buhari a 2023.

A yankin Kudu maso Yammacin Najeriya, tsohon gwamnan na Legas sananne ne wajen kitsawa da daura wasu fitattun 'yan siyasa a kujeru daban-daban, musamman gwamnoni.

Mutane da kungiyoyin dake tallafawa tafiyar Tinubu
Jerin 'Yan Siyasan Najeriya da Kungiyoyin Dake Yiwa Tinubu Gangamin 2023 | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Ba iya nan kadai ba, Tinubu na alfahari da ba wasu 'yan siyasa damar cimma burinsu na mulki a yankin nasu.

Hakazalika, Tinubu ba kanwar lasa bane a Arewa, domin kuwa an ce dashen bishiyarsa a yankin tuni sun yi jijiyoyi masu karfin da ba lallai a iya tumbuke su ba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A rahotonnan, mun tattaro muku jerin fitattun kungiyoyi, da ‘yan Najeriya, musamman ‘yan siyasa dake gangamin tallata tafiyar Bola Tinubu a zaben 2023 mai zuwa.

Jerin jiga-jigan 'yan Najeriya

 1. Mudashiru Obasa - Kakakin majalisar dokokin jihar Legas
 2. Hamisu Chidari - Kakakin majalisar dokokin jihar Kano
 3. Sanata Adesoji Akanbi - Tsohon sanatan Oyo ta Kudu,
 4. Adeseye Ogunlewe - Tsohon ministan ayyuka
 5. Oba Abdulrasheed Akanbi - Oluwo na Iwo a jihar Osun
 6. Abdulsalam Abdulkareem Zaura - Dan takarar gwamna a APC
 7. Joe Igbokwe - Jigon jam'iyyar APC
 8. Sanata Abu Ibrahim - Tsohon mataimakin shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawa
 9. Gwamna Babajide Sanwo-Olu na jihar Legas
 10. Farfesa Mohammed Kuta Yahaya - Tsohon sakataren gwamnatin jihar Neja (SSG)
 11. James Faleke - Dan majalisar wakilai ta kasa

Kungiyoyin da ke goyon bayan Tinubu

 1. Tinubu for President 2023
 2. Disciples of Jagaban
 3. Tinubu Grassroots Movement
 4. Asiwaju Bola Ahmed Tinubu – B.A.T National Forum
 5. Bola Ahmed Tinubu Group – USA
 6. Northern Alliance for Tinubu 2023
 7. Tinubu 2023 Support Group
 8. Tinubu Solidarity Group
 9. Tinubu Peoples Network
 10. Tinubu Transformation Agenda 2023
 11. I Love Tinubu
 12. Tinubu Mandate Group
 13. Asiwaju Ahmed Bola Tinubu Northerners
 14. Vote Tinubu 2023

'Yan a Mutun Tinubu Sun Dura Wani Asibiti a Abuja, Sun Tallafawa Marasa Lafiya

A wani labarin, wasu 'yan a mutun dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC Bola Tinubu, a ranar Alhamis, 1 ga watan Satumba, sun yi abin kirki ta hanyar biyawa majinyata 4o kudin magani a a babban asibitin Kubwa dake babban birnin tarayya, Abuja.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa masoyan na Tinubu sun yi wannan aikin ne a gaban Daraktan Likitoci, Dokta Lasisi Muyideen da wasu manyan ma’aikatan asibitin.

Da yake zantawa da manema labarai, Shola Olofin wanda ya shirya shirin tallafin kuma shugaban tawagar gangami ta Bola Ahmed Tinubu Vanguard ya bayyana kadan daga manufar wanna ba da tallafi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel