2023: Jerin Manyan Yan Kannywood 3 Da Ke Neman Takara A Jam'iyyar ADP

2023: Jerin Manyan Yan Kannywood 3 Da Ke Neman Takara A Jam'iyyar ADP

  • Gabannin zaben 2023, wasu manyan yan fim sun ayyana kudirinsu na neman takarar mukaman siyasa a karkashin jam'iyyar ADP a Kano
  • Daddy Hikima, Aminu Alan waka da Naziru Dan Hajiya za su nemi mukaman siyasa a karkashin jam'iyyar Sha'aban Sharada
  • A ranar Lahadi, 4 ga watan Satumba ne tsohon hadimin shugaban kasa, Sha'aban Ibrahim Sharada ya bayyana kudirinsa na neman kujerar gwamna

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kano - Manyan yan Kannywood da suka hada da Adam Abdullahi Adam wanda aka fi sani da Daddy Hikima, Aminu Ala da Naziru Dan Hajiya sun shiga takarar siyasa a zaben 2023.

Jaruman fim din za su yi takara ne a karkashin jam'iyyar Action Democratic Party (ADP) wanda a cikinta ne tsohon hadimin shugaban kasa, Sha'aban Ibrahim Sharada ke neman takarar gwamna.

Dan Hajiya, Ala, Daddy Hikima
2023: Jerin Manyan Yan Kannywood 3 Da Ke Neman Takara A Jam'iyyar ADP Hoto: nazir_danhajiya/alan_waka/daddyhikima
Asali: Instagram

Sharada dai ya ayyana kudirinsa na neman kujerar gwamna karkashin ADP ne a ranar Lahadi 4 ga watan Satumba a wani taro da aka gudanar a cibiyar matasa ta Sani Abacha da ke Kano.

Kara karanta wannan

Tsohon Hadimin Buhari Ya Shigo Takarar Gwamnan Kano Gadan-Gadan Daga Baya

Sai dai kuma, ana zargin mawakin siyasa, Dauda Kahutu Rarara ya watsar da tsohon ubangidansa, Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano sannan ya hade da Sharada.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Legit.ng Hausa ta tattaro bayanai game da jaruman fim din da ke neman takarar mukaman siyasa a 2023.

1. Daddy Hikima

Jarumi Adam Abdullahi Adam wanda aka fi sani da Daddy Hikima yana neman takarar kujerar dan majalisa mai wakiltan mazabar Kumbotso a karkashin jam'iyyar ADP.

Koda dai mutane da dama na sukar yadda yake fitowa a matsayin dan daba a fina-finai, Abale wanda ya kasance haifaffen dan karamar hukumar Kumbotso na daya daga cikin jaruman da ake yawan magana kansu a masana'antar.

Ya fito a fina-finai da dama kamar su A duniya, Haram, Iyyali Na, Labarina, Farin Wata, Na Ladidi, Sanda da sauransu.

2. Aminu Ladan Abubakar (Ala)

Kara karanta wannan

Hotuna: Kwankwaso Ya Ziyarci Jihar Benue, Ya Aiwatar Da Muhimmin Aiki

Aminu Ladan Abubakar wanda aka fi sani da Alan waka yana neman takarar dan majalisa mai wakiltan mazabar Nasarawa a majalisar tarayya.

Ala wanda ya kasance haifaffen Yakasai, birnin Kano, yayi fice sosai a duniyar mawakan Hausa kuma ya rubuta litattafai da dama da suka hada da Cin Zarafi, Bakar Aniya, Sawaba, Cin Fuska, Jirwaye, Tarzoma.

Mawakin ya yi karatu a jami'o'i da dama a ciki da wajen Najeriya.

3. Nazir Dan Hajiya

Shahararren furodusa, Naziru Dan Hajiya na neman takarar kujerar dan majalisar tarayya mai wakiltan mazabar Kura/Garun Malam.

Jarumin wanda aka haifa a garin Jos, jihar Filato, ya jagoranci shirya fina-finai kimanin guda 20 zuwa 30 da suka hada Bahaushiya, Baya da Kura, Gamdakatar, Halisa, Hijira, Al’ajabi, da sauransu.

Tsohon Hadimin Buhari Ya Shigo Takarar Gwamnan Kano Gadan-Gadan Daga Baya

A gefe guda, mun dai ji cewa tsohon Mai ba shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara, Hon. Sha’aban Ibrahim Sharada ya fito takarar gwamna a jam’iyyar ADP.

Kara karanta wannan

An Fara Sauraron Karar da Aka Kai Domin Karbe Takaran PDP Daga Hannun Atiku

Rahoton Daily Trust yace Honarabul Sha’aban Ibrahim Sharada ya shaidawa mutanen Kano burinsa da ya ayyana niyyar neman Gwamna.

An yi wani taro a cibiyar matasa ta Sani Abacha Youth a Kano a ranar Lahadi, 4 ga watan Satumba 2022, inda ‘dan takaran ya nuna ga gaske yake yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel