Hotuna: Kwankwaso Ya Ziyarci Jihar Benue, Ya Aiwatar Da Muhimmin Aiki

Hotuna: Kwankwaso Ya Ziyarci Jihar Benue, Ya Aiwatar Da Muhimmin Aiki

  • Jihar Benue ta cika ta tumbatsa yayin da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NNPP ya kai ziyara jihar
  • Kwankwaso ya kaddamar da ofishin yakin neman jam'iyyarsa ta NNPP gabannin zaben 2023
  • Tsohon gwamnan na jihar Kano na daya daga cikin manyan takarar da ke hararar kujerar Buhari a zabe mai zuwa

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Benue - Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya kaddamar da ofishin yakin neman zaben jam’iyyar a jihar Benue.

Bikin kaddamar da ofishin wanda ya gudana a yau Asabar, 4 ga watan Satumba, ya samu halartan mutane masu yawan gaske.

Kwankwaso a taro
Hotuna: Kwankwaso Ya Ziyarci Jihar Benue, Ya Aiwatar Da Muhimmin Aiki Hoto: @SaifullahiHon
Asali: Twitter

A cikin wata wallafa da Saifullahi Hassan, hadimin Kwankwaso ya yi a shafinsa na Twitter, ya bayyana cewa dan takarar shugaban kasar ya samu rakiyar manyan jiga-jigan jam’iyyar a jihar.

Kara karanta wannan

2023: Peter Obi Zai Rasa Takarsa Na Shugaban Kasa A Labour Party? Sabbin Bayanai Sun Fito Fili

Daga cikin wadanda suka yi masa rakiya akwai dan takarar gwamna na jam’iyyar a jihar, Farfesa Ben Angwe, shugaban jam’iyyar a jihar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sauran sun hada da yan takarar kujerar sanata, masu neman takarar kujerun yan majalisar wakilai da sauransu.

Gaskiyar Abinda Ya Faru Game Da Ruwan Jifan Da Aka Yiwa Kwankwaso A Jihar Kogi

A wani labarin, kungiyar yakin neman zaben Rabiu Musa Kwankwaso ta yi watsi da rahoton cewa yan iskan gari sun jefi dan takarar shugaban kasar na jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) a jihar Kogi.

Mun ji a baya cewa wasu da ake zargin yan jagaliya ne sun jefi Kwankwaso da ledojin ruwa yayin da ya kai ziyara jihar.

Kwankwaso dai ya je Lokoja, babban birnin jihar ta Kogi don kaddamar da sakatariyar jam’iyyar da ofishoshin kamfen dinsa.

Kara karanta wannan

Gaskiyar Abinda Ya Faru Game Da Ruwan Jifan Da Aka Yiwa Kwankwaso A Jihar Kogi

Asali: Legit.ng

Online view pixel