Rikicin PDP: Wike, Ortom Da Wasu Gwamnonin PDP Sun Sake Dunguma Sun Tafi Landan

Rikicin PDP: Wike, Ortom Da Wasu Gwamnonin PDP Sun Sake Dunguma Sun Tafi Landan

  • Har yanzu dai an gaza kawo karshen rikicin da ke tsakanin dan takarar shugaban kasa na PDP Atiku Abubakar da Gwamna Nyesom Wike
  • Wike da wasu gwamnonin jam'iyyar PDP da ke goyon bayansa sun sake kama hanya sun bazama su birnin Landan a Birtaniya don yin taro
  • Wata majiya kwakwara ta ce Wike da gwamnonin da ke goyon bayansa za su yi taron ne don tattauna matakin da za su dauka kafin kafa kwamitin kamfen na zaben 2023

Bayan gaza yin sulhu tsakanin dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP Atiku Abubakar da bangaren gwamna Nyesom Wike na Jihar Rivers, gwamna da wasu makusantansa sun koma Landan don yin wasu taruruka.

Atiku ya gana da Wike da wasu makusantansa a Landan makonni biyu da suka wuce. Dan takarar shugaban kasar, kamar yadda aka rahoto ya yi magana da gwamnonin kan bukatar su tunkari zaben 2023 a matsayin tsintsiya madaurin ki daya.

Kara karanta wannan

PDP: Yadda Shettima Yayi Zagon Kasa ga Kokarin Jonathan na Ceto 'Yan matan Chibok

Wike and Govs
Rikicin PDP: Wike, Ortom Da Makinde Sun Koma Landan Don Yin Wasu Tarurrukan. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Amma, bayan hakan Wike da Sanata Iyoricha Ayu, shugaban PDP na kasa, sun cigaba da musayar maganganu a shafukan kafafen watsa labarai.

Makasudin yin taron na Landan - Majiya

Daily Trust ta gano daga majiya kwakwara cewa za a yi taron na Landan ne don tsare-tsare gabanin taron kwamitocin NEC da NWC kafin kafa majalisar kamfen din PDP.

Taron na Landan kamar yadda Daily Trust ta fahimta za a yi shi ne don yanke shawarar ko bangaren Wike za ta amshi wani mukami a majalisar ta kamfen din.

Wata majiya ta shaidawa Daily Trust cewa bayan taron da dan takarar shugaban kasar Atiku Abubakar, bangarorin biyu na sa ran za a yi sulhu.

Majiyar ta ce:

"Bangaren Wike na fatan Atiku zai shawo kan shugaban jam'iyyar PDP na kasa Ayu ya sauka daga mukaminsa. Amma abubuwan da suka faru a kwanakin nan sun canja lissafin. Tamkar bangarorin biyu ba su hakura ba. Ina ganin za su sake shiri ne kuma su yanke shawara kan rawar da za su taka a majalisar ta kamfen."

Kara karanta wannan

Gwamna Wike Karamin Yaro Ne: Shugaban PDP, Iyorchia Ayu, Ya yi Raddi

Atiku Ya Yi Kus-Kus Da Yan Takarar Gwamna Na Jam'iyyar PDP A Gidansa Da Ke Abuja

A bangare guda, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar, a ranar Asabar ya gana da yan takarar gwamna na jam'iyyar daga jihohin Najeriya.

Tsohon mataimakin shugaban kasar tare da abokin takararsa, Gwamna Ifeanyi Okowa na Jihar Delta, sun gana da yan takarar a gidansa da ke Asokoro, birnin tarayya Abuja.

Wadanda suka hallarci taron akwai yan takarar gwamna daga jihohin Kaduna, Plateau, Katsina, Legas, Niger, Kano, Sokoto, Delta, Yobe, Jigawa, Nasarawa, Kwara, Benue, Ebonyi da Zamfara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel