PDP: Yadda Shettima Yayi Zagon Kasa ga Kokarin Jonathan na Ceto 'Yan matan Chibok

PDP: Yadda Shettima Yayi Zagon Kasa ga Kokarin Jonathan na Ceto 'Yan matan Chibok

  • Jam'iyyar PDP ta zargin Sanata Kashim Shettima da yin zagon kasa wurin kokarin Jonathan na ceto 'yan matan Chibok
  • Kamar yadda kakakkin jam'iyyar ya fitar, yace Tinubu da Shettima na kokarin tsame kansu daga gazawar mulkin Buhari
  • A cewarsa, akwai abubauwan da 'yan Najeriya ba zasu manta ba duk da Tinubu da Shettima na cusa kansu wurin Jonathan mai kishin kasa

FCT, Abuja - Jam'iyyar PDP ta caccaki 'dan takarar mataimakin shugaban kasa na APC, Kashim Shettima kan yadda yake kokarin yin gogayyar suna da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan bayan zarginsa da ake da zagon kasa ga gwamnatin Jonathan wurin shawo kan matsalar tsaro a Borno.

Shettima shi ne gwamnan jihar Borno daga watan Mayun 2011 zuwa Mayun 2019 yayin da Jonathan yake shugaban kasa tsakanin 2010 zuwa 2015.

Kara karanta wannan

Tsohon Minista Ya Bayyana Halin da Lafiya 'Dan Takarar APC, Bola Tinubu, Take Ciki

Jonathan da Tinubu
PDP: Yadda Shettima Yayi Zagon Kasa ga Kokarin Jonathan na Ceto 'Yan matan Chibok. Hoto daga @bong_umar
Asali: Twitter

Shettima da 'dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Bola Tinubu, a cikin makon nan sun halarci shaglin zagayowar ranar haihuwar Mathew Kukah na 70 inda suka dinga kashe hotunan da malamin addinin Kiristancin.

Amma sakataren yada labarai na jam'iyyar PDP, Debo Ologunagba a takardar da ya fitar a ranar Alhamis, ya caccaki su biyun inda yace abun kunya da munafunci suka yi ta yadda suke zagin Jonathan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Channels TV ta rahoto cewa, mai magana da yawun jam'iyyar PDP ya kara da cewa, abun kunya ne yadda Tinubu da Shettima a halin yanzu suke nisanta kansu da gazawar shugaban kasa Muhammadu Buhari.

"A kokarin gyarawa tare da wanke bataccen sunansu, alakanta kansu da nasarar PDP da kuma kokarin fitar da mutum nagari a Kashim Shettima, sauran shugabannin APC babu kunya sun yi amfani da dama wurin yin hoto da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan na jam'iyyar PDP.

Kara karanta wannan

Gwamna Wike Karamin Yaro Ne: Shugaban PDP, Iyorchia Ayu, Ya yi Raddi

“Wannan shugaban Najeriya ne mai kishin kasa wanda yayi mulki cike da nasarar inda APC sjuka dinga zagi, zagon kasa, hantara da suka don son mulki," wani sashin takardar yace.
"'Yan Najeriya basu manta yadda Aiswaju Tinubu ya dinga zagin Jonathan ba yana watsa kalaman tsana ga mulkinsa kuma har ya dauka nauyin zanga-zangar wacce aka shirya kan karairayin tattalin arziki, farfaganda da karya don bata sunan mulkin Jonathan.
“'Yan Najeriya zasu tuna yadda Sanata Shettiima matsayinsa na gwamnan Borno ya dinga zagon kasa tare da hana gwamnatin Jonathan shawo kan matsalar tsaro a Borno," takardar tace.

Takardar ta kara da bayyana cewa:

"Har yanzu ana tuna yadda 'dan takarar mataimakin shugaban kasan APC ya ki aiki da rahoton tsaro tare da umartar a rufe makarantun kauyukan Borno tare da kwashe dalibai masu rubuta GCE har aka sace su a Chibok.
“'Yan Najeriya zasu tuna yadda Gwamna Shettima ya kange mataimakinsa, babban jami'in tsaro jihar tare da rike muhimman bayanan tsaro don goyon bayan 'yan ta'adda, hakan yasa aka kasa ceto 'yan matan Chibok."

Kara karanta wannan

Atiku ya ce zai siyar da kamfanin man fetur idan ya gaji Buahri, ya fadi wadanda za su siya

Rushewar Ginin Kano: Tinubu ya Aike wa Ganduje Wasikar Jaje

A wani labari na daban, 'dan takarar kujerar shugabancin kasa karkashin jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya jajanta wa gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, kan rayukansu da aka rasa a rushewar gini mai hawa uku na kasuwar Beirut a jihar.

Daily Trust ta ruwaito cewa, a wasikar da Tinubu ya rubuta zuwa Gwamna Ganduje mai kwanan wata 31 ga Augustan 2022, ya bayyana matukar damuwarsa da tausayawa kan mummunan al'amarin da ya faru.

Ya kara da yi wa wadanda suka samu rauni fatan samun lafiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel