Gwamna Wike Karamin Yaro Ne: Shugaban PDP, Iyorchia Ayu, Ya yi Raddi

Gwamna Wike Karamin Yaro Ne: Shugaban PDP, Iyorchia Ayu, Ya yi Raddi

  • Karon farko, Shugaban uwar jam'iyyar PDP ya mayar da martani da Gwamna Nyesom Wike
  • Ayu Iyorchia ya lashi takobin cewa sam ba zai yi murabus daga kujerarsa ba kuma ko a jikinsa
  • An samu baraka cikin Jam'iyyar PDP tun bayan zaben dan takarar kujerar mataimakin shugaban kasa

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Shugaban uwar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Iyorchia Ayu, ya ce masu kira ga yayi murabus daga kujerarsa kananan yara ne basu nan lokacin da aka kafa jam'iyyar.

Gwamna Wike da mabiyansa ne ke kira ga Shugaban PDP, Ayu, yayi murabus a matsayin sharadin marawa takarar Atiku goyon baya.

Wannan abu ya hargitsa rikici a cikin babbar jam'iyyar ta adawa.

Alhaji Atiku Abubakar ya kayar da Wike a zaben fidda gwanin jam'iyyar PDP.

Duk da an bukaci Atiku ya zabi Wike matsayin mataimaki, ya zabi gwamnan Delta, Ifeanyi Okowa.

Kara karanta wannan

2023: Gwamna Wike Ya Yi Martani Ga Wasu Jiga-Jigan PDP, Ya Bayyana Aikin Da Yake Wa APC

Masu goyon bayan Wike sunce ba zai yiwu dan takarar shugaban kasa da shugaban jam'iyya su kasance daga yankin Arewa ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Amma yayin hira da sashen Hausa na BBC, Ayu ya ce su Wike basu da wayau lokacin da suka yi gwagwarmayar kafa jam'iyyar.

Ayu yace sam ko a jikinsa maganar cewa yayi murabus.

Ayu Iyorchia
Gwamna Wike Karamin Yaro Ne: Shugaban PDP, Iyorchia Ayu, Ya yi Raddi Hoto: Official PDP
Asali: Twitter

Ya cewa a lokacin da aka gudanar da zaben shugabannin PDP, an yi ittifakin cewa ba za a yi la'akari da yankin da shugaban jam’iyyar ya fito ba wurin zaben dan takarar shugaban kasar.

Ayu yace:

''Maganar zaben Atiku ba ta shafi mukamin Shugaban jam'iyya ba. Ni na ci zabe. A cikin kundin tsarinmu muka yi wannan.'
''Ba wani laifi da na yi, ina gyara jam'iyya ne, hayaniyar da ake yi wallahi ba ta dame ni ba."

Kara karanta wannan

Shugaban Jam’iyya Ya Yarda Akwai Rikici a PDP, Ya Hango Abin da Zai Faru a 2023

''Lokacin da muka fara tafiyar PDP wadannan yara bamu gan su ba. Su yara ne basu san abunda yasa muka kafa wannan jam'iyyar ba."
"Ba za mu yarda mutum daya ya zo ya lalata mana jam'iyya ba,'' a cewar Ayu.

Gwamna Wike Ya Sake Martani Kan Rikicin PDP, Ya Faɗi Aikin Da Zai Wa APC

Gwamna Nyesom Wike ya caccaki jiga-jigan PDP dake sukarsa, inda ya bayyana cewa a lokacin da suka maida hankali kan kalamai mara dadi, shi kuma yana kokarin ganin bayan APC a Ribas.

A ranar Litinin da ta gabata, Wike ya yi ikirarim cewa babu wanda zai razana shi domin zai yi duk abinda ya natsu cewa dai-dai ne ko da kuwa za'a masa taron dangi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel