Atiku Ya Yi Kus-Kus Da Yan Takarar Gwamna Na Jam'iyyar PDP A Gidansa Da Ke Abuja

Atiku Ya Yi Kus-Kus Da Yan Takarar Gwamna Na Jam'iyyar PDP A Gidansa Da Ke Abuja

  • Alhaji Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party a zaben shekarar 2023 ya yi taro da yan takarar gwamna na jam'iyyar a Abuja
  • Atiku ya ce ya kira taron ne domin su tattauna matsalolin da ke adabar Najeriya da kuma hanyoyin da za su hada kan yan Najeriya don kwace mulki daga hannun APC a 2023
  • Wannan taron na Atiku da yan takarar gwamna na PDP na zuwa ne a lokacin da Gwamna Wike da wasu takwarorinsa na jam'iyyar suka sake shillawa Landan don yin wasu tarurukan

FCT Abuja - Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar, a ranar Asabar ya gana da yan takarar gwamna na jam'iyyar daga jihohin Najeriya.

Tsohon mataimakin shugaban kasar tare da abokin takararsa, Gwamna Ifeanyi Okowa na Jihar Delta, sun gana da yan takarar a gidansa da ke Asokoro, birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Allah Yayi wa Tsohon Jakadan Najeriya a Kasar Saudi Arabia, Imam, Rasuwa

Atiku and PDP Candidates
Hotuna: Atiku Ya Yi Taro Da Yan Takarar Gwamna Na PDP A Abuja. Hoto: @atiku.
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wadanda suka hallarci taron akwai yan takarar gwamna daga jihohin Kaduna, Plateau, Katsina, Legas, Niger, Kano, Sokoto, Delta, Yobe, Jigawa, Nasarawa, Kwara, Benue, Ebonyi da Zamfara.

An yi taron ne a cikin sirri.

Sai dai bayan taron, Atiku ya wallafa hotunansa da mahallarta taron a shafinsa na Twitter.

Atiku da yan takarar gwamnoni na PDP
Hotuna: Atiku Ya Yi Taro Da Yan Takarar Gwamna Na PDP A Abuja. Hoto: @atiku.
Asali: Twitter

Atiku da yan takarar PDP
Hotuna: Atiku Ya Yi Taro Da Yan Takarar Gwamna Na PDP A Abuja. Hoto: @atiku.
Asali: Twitter

Atiku da yan takarar PDP
Hotuna: Atiku Ya Yi Taro Da Yan Takarar Gwamna Na PDP A Abuja. Hoto: @atiku.
Asali: Twitter

Sai dai bayan taron, Atiku ya wallafa hotunansa da mahallarta taron a shafinsa na Twitter.

A sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Atiku ya ce:

"Yau na gana da yan takarar gwamna na jam'iyyar PDP a gida na da ke Abuja. Dama ce na tattaunawa kan halin da kasa ke ciki da yadda za mu hada kan yan Najeriya don aikin da ke gabanmu na fatattakar jam'iyya mai mulki da fara sake gina Najeriya - AA."

Kara karanta wannan

An Fara Sauraron Karar da Aka Kai Domin Karbe Takaran PDP Daga Hannun Atiku

Rikicin PDP: Wike, Ortom Da Wasu Gwamnonin PDP Sun Sake Dunguma Sun Tafi Landan

A wani rahoton, kun ji cewa bayan gaza yin sulhu tsakanin dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP Atiku Abubakar da bangaren gwamna Nyesom Wike na Jihar Rivers, gwamna da wasu makusantansa sun koma Landan don yin wasu taruruka.

Atiku ya gana da Wike da wasu makusantansa a Landan makonni biyu da suka wuce. Dan takarar shugaban kasar, kamar yadda aka rahoto ya yi magana da gwamnonin kan bukatar su tunkari zaben 2023 a matsayin tsintsiya madaurin ki daya.

Amma, bayan hakan Wike da Sanata Iyoricha Ayu, shugaban PDP na kasa, sun cigaba da musayar maganganu a shafukan kafafen watsa labarai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel