Jerin Kananan Hukumomi 40 a Najeriya da Ba Lallai a Yi Zabe Ba a 2023

Jerin Kananan Hukumomi 40 a Najeriya da Ba Lallai a Yi Zabe Ba a 2023

 • Kananan hukumomi 40 ne akalla ake yawan kai farmaki a wasu jihohin Najeriya, kuma akwai alamun ba lallai su kada kur'u a zabe mai zuwa ba saboda ta'azzarar lamarin tsaro
 • Jihohin da hakan ya shafa irinsu Kaduna da Zamfara da Imo da Neja da kuma Sokoto ne, kasancewar 'yan ta'adda sun tasa yankunan a gaba
 • Duk da haka, gwamnatin Buhari na kara lasa ma jama'a zuma a baki cewa tabbas za a yi zabe a kowane yankin kasar nan

Najeriya - Ta'azzarar rashin tsaro a Najeriya ya sa 'yan kasar da dama cikin tashin hankali, kuma kullum tsoro karuwa yake a zukatan wasu da dama.

Jaridar Punch, ta ruwaito cewa, akwai kananan hukumo sama da 40 da ba lallai su kada kuri'u ba a zabe mai zuwa saboda yawaitar harin 'yan ta'adda.

Kara karanta wannan

Yajin Aiki: Ɗan El-Rufai Ya Ce ASUU 'Bata Da Amfani', An Masa Zafafan Martani

Kananan hukumomi 40 da ba lallai a yi zabe ba a 2023
Jerin kanan hukumomi 40 a Najeriya da ba lallai a yi zabe ba a 2023 | Hoto: Hope Uzodimma, Nasir El-Rufai, Bello Matawalle, Aminu Tambuwal
Asali: UGC

Kananan hukumomin 40 suna karkashin fadin jihohin Kaduna, Zamfara, Niger, Katsina, Abia da Imo ne, kuma ga su kamar haka:

'Yan bindiga sun mamaye kananan hukumomi 8 a Kaduna

 1. Chikun
 2. Kajuru
 3. Kachia
 4. Zangon Kataf
 5. Kauru
 6. Lare
 7. Birnin Gwari
 8. Giwa

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

'Yan ta'adda da 'yan bindiga sun karbe kananan hukumomi 9 a Zamfara

 1. Maru
 2. Tsafe
 3. Bakura
 4. Anka
 5. Maradun
 6. Gusau
 7. Bukkuyum
 8. Shinkafi
 9. Bungudu

Boko Haram da sauran 'yan ta'adda sun kama kananan hukumomi 7 a Neja

 1. Rafi
 2. Munyan
 3. Shiroro
 4. Magama
 5. Mashegu
 6. Mariaga
 7. Wushishi

Kananan hukumomi 11 cikin 23 na Sokoto na fama hare-hare

 1. Illela
 2. Rabbah
 3. Sabon-Birni
 4. Isa
 5. Wurno
 6. Gada
 7. Goronyo
 8. Tangaza
 9. Gudu
 10. Denge-Shuni
 11. Kebbe

Kara karanta wannan

Rundunar Sojin Najeriya Ta Yanke Hukunci Kan Sojojin da Suka Kashe Sheikh Goni a Jihar Yobe

Kanan hukumo 5 da 'yan bindiga suka addaba a jihar Imo

 1. Orsu
 2. Orlu
 3. Oru East
 4. Oru West
 5. Njaba

Ba Lallai a Yi Zabe a Wasu Jihohin Arewa Maso Yamma Ba, Inji Gwamnonin Najeriya Ga Buhari

A wani labarin, wani sabon batu ya fito daga bakin gwamnonin Najeriya, inda suka bayyana ra'ayin cewa ba lallai a yi zabuka a wasu jihohin Arewa maso Yammacin kasar nan ba saboda kara dagulewar lamarin tsaro a shiyyar.

Arewa maso Yammancin Najeriya dai ta ta kunshi jihohi bakwai da suka hada da; Jigawa, Kaduna, Kano, Katsina, Kebbi, Sokoto, da Zamfara.

Jaridar TheCable ta ruwaito cewa, gwamnonin sun bayyanawa Buhari hakan ne a wani taron kan samar da wasu ka'idoji.

Asali: Legit.ng

Online view pixel