Rundunar Soji Ta Kori Sojoji Biyu Kan Kisan Sheikh Goni Aisami a Yobe

Rundunar Soji Ta Kori Sojoji Biyu Kan Kisan Sheikh Goni Aisami a Yobe

  • Rundunar sojin Majeriya ta kori sojoji biyu da ake zargi da kisan Sheikh Goni Aisami Gashuwa a jihar Yobe
  • Kwamitin da rundunar soji ta kafa domin gudanar da bincike kan lamarin ya kammala aikinsa
  • Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari, ya yi Allah wadai da kisan Malamin kuma ya ba da umarnin a hukunta masu laifin

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Yobe - Hukumar Sojin Najeriya ta sallami Sojojinta guda biyu daga aiki kan kisan babban Malamin addinin Musulunci, Sheikh Goni Aisami Gashuwa, a jihar Yobe.

Channels tv ta ruwaito cewa sojojin da korar ta shafa sun haɗa da, Lance Kofur John Gabriel da kuma Lance Kofur Adamu Gideon.

Sojin da suka kashe Sheikh a Yobe.
Rundunar Soji Ta Kori Sojoji Biyu Kan Kisan Sheikh Goni Aisami a Yobe Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Muƙaddashin kwamandan Bataliya ta 241 da ke sansani a Nguru, jihar Yobe, Laftanar Kanal Ibrahim Osabo, ya shaida wa ƴan jarida cewa kwamitin binciken da aka kafa da haɗin kan yan sanda ya kama su da aikata laifin kisan.

Kara karanta wannan

Hotuna: An Bude Katafaren Masallacin Kaltungo, jihar Gombe Ranar Juma’a

Kwamandan ya ce Sojin guda biyu sun rasa aikin su ne bisa aikata laifuka biyu, gaza sauke nauyin dake kansu da kuma saɓa wa tanadin aikin soji.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Osabo ya kara da cewa za su miƙa sojojin biyu ga hukumar ta kora ga hedkwatar ƴan sanda da ke Damaturu, babban birnin jihar Yobe, domin gurfanar da su a Kotu doka ta yi aiki a kansu.

Kisan Sheikh Gashuwa

Idam baku manta ba, Legit.ng Hausa ta kawo muku rahoton yadda wani Soja ya kashe Sheikh Goni Gashuwa daga rage masa hanya.

Bayaani sun nuna cewa Malamin na kan hanyarsa ta zuws Gashuwa daga Kano yayin da wanda ake zargin ya yi ajalinsa.

Wasu daga cikin mazauna garin Gashuwa sun bayyana cewa lamarin ya auku a Jaji Maji, kilomita 30 daga garin Gashuwa, mahaifar shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Bayan Kwanaki 30 a Tsare, An Sako Shahrarren Lauya Daga Kurkuku

Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya yi Allah wadai da lamarin, tare da umartar hukumar soji ta ɗauki mataki kan waɗan da ake zargi.

A wani labarin kuma Sanata Ahmad Lawan ya ce Majalisar dattawa ba zata zuba ido ba, zata bibiyi lamarin kashe Malamin har sai an hukunta Sojan

Majalisar Dattawa ta nemi mahukunta su gaggauta daukar mataki kan sojan da ya kashe Sheikh Goni Aisami Gashuwa jihar Yobe.

Shugaban majalisar, Sanata Ahamad Lawan, shi ne ya yi wannan kiran yayin da ya je ta'aziyya gidan marigayin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel