Yajin Aiki: Ɗan El-Rufai Ya Ce ASUU 'Bata Da Amfani', An Masa Zafafan Martani

Yajin Aiki: Ɗan El-Rufai Ya Ce ASUU 'Bata Da Amfani', An Masa Zafafan Martani

  • Bashir El-Rufai, daga daga cikin yayan gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya yi magana kan tsawaita yajin aiki da kungiyar ASUU ta yi
  • Bashir ya bayyana kungiyar ta malaman jami'o'i a matsayin mara amfani kuma ya bada shawarar a soke kungiyar a maye gurbinta da masu kishin dalibai da ilimi
  • Wannan kalaman na dan tsohon ministan na babban birnin tarayya Abuja ta harzuka wasu masu amfani da dandalin sada zumunta inda suka rika masa martani

Twitter - Daya cikin 'ya'yan Gwamna Nasir El-Rufai na Jihar Kaduna, ya janyo cece-kuce a dandalin sada zumunta bayan ya kira kungiyar ASUU 'kungiya mara amfani'.

ASUU, a ranar Litinin, ta tsawaita yajin aikinta na tsawon wata shida zuwa har sai baba ta gani, tana mai cewa ba za ta janye ba sai gwamnatin tarayya ta biya mata bukatunta.

Kara karanta wannan

Babban gaye: Yadda nau'in takalmin wani dan kwalisa ya girgiza mutane a intanet

Bashir El-Rufai
An Huro Wa Ɗan El-Rufai Wuta Kan Cewa ASUU 'Bata Da Amfani'. Hoto: @BashirElRufai.
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da ya ke martani kan tsawaita yajin aikin, dan gwamnan cikin rubutun da ya wallafa a shafinsa na Twitter ya ce:

"Ya kamata a soke kungiyar a maye gurbinta da malamai wadanda suka damu da dalibai dda kuma yadda hakan zai kawo cigaba a kasar."

Martanin wasu daga cikin masu amfani da shafukan sada zumunta

@alex_obella:

"Bashir zai iya furta hakan, tunda ba shi da matsala yana morar kudin 'yan kasa ne duk rayuwarsa."

@revelationnahua:

"Ya kula da abin da ya ke fada ... zamansa dan gwamnan Kaduna baya nufin kai kadai za ka iya magana kan ASUU da sauran yan kasa. Idan ka fada kalmar kiyayya, za ka gurfana a kotu."

@cosmopolitan40:

"Mugu Bashir, ban ga laifin ka ba. Me za ka ce? Ba wani abu mai muhimmanci, ka yi karatu a daya cikin jami'u mafi kyau a kasar waje da kudin al'umma. Malam ...".

Kara karanta wannan

Yanzun nan: ASUU ta gama tattaunawa a Abuja, ta sake fitar da matsaya

Wani mai amfani da Facebook, Adeyeye Oluwatosin ya ce:

"Ya ce ASUU bata da amfani, duk da ya san mahaifinsa na daya ciin wadanda suka sa ASUU ta lalace yana nufin mahaifinsa ya ci kungiyar lalacewa."

Thompson Ewedoma ya rubuta:

"Wawa ne, ban san abin da ya bashi kwarin gwiwar furta hakan ba."

Tun a watan Fabrairun 2022 ASUU ta fara yajin aikin sati hudu don neman biya musu bukatunsu, amma suka tsawaita yajin aikin bayan gwamnati ta gaza yi musu abin da suke so.

Zuwa ranar Litinin, an shafe kimanin kwana 196 ana yajin aikin.

Yajin Aikin ASUU: Ba Dole Ne Sai Kowa Ya Yi Digiri Ba, In Ji Gwamnan APC

A wani rahoton, gwamnan Jihar Ebonyi kuma shugaban kungiyar gwamnonin Kudu maso Gabas, David Umahi ya ce ilimin Jami'a fa ba na kowa da kowa bane, rahoton The Punch.

Umahi ya jadada cewa ba adalci bane a yi tsammanin gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta ciyo bashin fiye da Naira tiriliyan 1 don biyan bukatun ASUU.

Kara karanta wannan

Babu Kudi A Harkar Fim: Jarumin Fim Ya Nemi EFCC Da NDLEA Su Binciki Jarumai Maza Da Ke Siyan Manyan Gidaje

Asali: Legit.ng

Online view pixel