Yanzu-Yanzu: Kotun Daukaka Kara Ta Tabbatar da Cire Dan a Mutun Kwankwaso Daga Shugabancin PDP a Kano

Yanzu-Yanzu: Kotun Daukaka Kara Ta Tabbatar da Cire Dan a Mutun Kwankwaso Daga Shugabancin PDP a Kano

  • Kotun daukaka kara a babban birnin tarayya Abuja ya yi watsi da hukuncin da babban kotun tarayya ya yanke
  • Jam'iyyar PDP ta ruguza shugabanci a jihar Kano, lamarin da kai bangarori suka kai gaban kotu neman hakki
  • A hukuncin da aka yanke a baya, an ba Shehu Sagagi umarnin ci gaba da shugabancin PDP, yanzu kuma kotun daukaka kara ya watsar da batun

FCT, Abuja - A yau Litinin 29 ga watan Agusta ne kotun daukaka kara da ke zamanta a Abuja ta aje hukuncin babbar kotun tarayya da ta ba Shehu Sagagi shugabancin jam’iyyar PDP na Kano.

Sagagi dai an ce dan a mutun Kwankwaso ne, kuma tsohon gwamnan ne ya yi ruwa da tsaki wajen ba shi shugaban jam'iyyar a jihar, Daily Nigerian ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Yanzun nan: Kotun daukaka kara ta mayarwa wani dan takarar gwamnan PDP tikitinsa

Bayan komawar Kwankwaso NNPP, ana zargin Sagagi da ci gaba da bin tafarki mai gidan nasa, alamrin da ka iya kawo tsaiko ga makomai siyasar PDP.

Kotu ta tabbatar da ruguza shugabancin PDP a jihar Kano
Yanzu-Yanzu: Kotun Daukaka Kara Ta Tabbatar da Cire Dan a Mutun Kwankwaso Daga Shugabancin PDP a Kano | Hoto: pmnewsnigeria.com
Asali: UGC

A ranar 29 ga watan Maris ne kwamitin NWC na PDP ya ruguza shugabancin jam’iyyar a Kano tare da nada kwamitin rikon kwarya na mutum shida a matsayin wanda zai maye gurbin shugabancin jam'iyyar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hukuncin kotun babban birnin tarayya

Mai shari'a Taiwo Taiwo ya umarci hedikwatar PDP da ta dakata da batun tsige Sagagi daga mukaminsa har sai ya gama wa’adinsa a watan Disamban 2024.

Mai shari’a Taiwo ya kuma bayyana cewa, NWC ko wani kwamitin jam’iyyar ba su da 'yancin tsige shugaba a wata jihar da aka kada kuri'u a tarukan gangami.

Sai dai, kotun daukaka kara ta watsar da batun mai shari’a Taiwo, inda ta yi tsokaci da cewa, batun cikin gida ne na jam'iyya, kuma PDP na da hurumin tsige shugabanta a kowace jiha.

Kara karanta wannan

Kano: 'Yan Daba Sun Kone Gidan 'Yan Shi'a, Kadarorin N3m Sun yi Kurmus

Bayanin hukuncin kotun daukaka kara

Kwamitin na kotun daukaka kara na mutum uku, kuma karkashin jagorancin mai shari’a Peter Ige, ya yi ittifakin cewa matakin da kwamitin NWC na PDP daidai ne.

Hakazalika, kwamitin ya ce babu mai kalubalantar batun nada kwamitin riko a Kano don ci gaba da kula da lamurran jam'iyyar kamar yadda NWC ya yi.

A bangare guda, ya ce taba wannan kwamiti na rikon kwarya ya sabawa kundin tsarin mulkin jam'iyyar PDP.

Shekarau ya yi alkawarin kawo kuri'un Kano da sauran jihohi ga Atiku a zaben 2023

A wani labarin, bayan sake zama mamba a jam'iyyar PDP, Mallam Ibrahim Shekarau ya dauki alkawurra ga dan takarar shugaban na jam'iyyar PDP.

A yau Litinin 29 ga watan Agusta ne tsohon gwamnan jihar Kano, kuma sanatan Kano ta tsakiya, Ibrahim Shekarau ya sake shiga inuwar jam’iyyar adawa ta PDP bayan ya shafe 'yan watanni da 'yan kayan marmari a NNPP.

Kara karanta wannan

Yajin aiki: ASUU ta shawarci Buhari kan yadda za a kawo karshen yajin aiki

Shekarau ya shiga NNPP ne tare da 'yan a mutunsa bayansa a ranar 18 ga watan Mayu, biyo bayan dambarwar da ta barke tsakaninsa da gwamnan Kano na yanzu; Abdullahi Ganduje kan rikon shugabancin APC a jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel