Kotun Daukaka Kara Ta Soke Batun Kwace Tikitin Oborevwori a Matsayin Dan Takarar Gwamnan Delta Na PDP

Kotun Daukaka Kara Ta Soke Batun Kwace Tikitin Oborevwori a Matsayin Dan Takarar Gwamnan Delta Na PDP

  • Bayan duba da tsanaki, kotun daukaka kara a babban birnin tarayya Abuja ta soke wani hukuncin babban kotun tarayya
  • An yi zaben fidda gwanin PDP a ranar 25 ga watan Mayu, Oborevwori ya lashe zabe da kuri'u sama da 500
  • A ranar Litinin, jam'iyyar PDP ta samu karuwa, jigon siyasa a jihar Kano ya karbi kalmar shiga PDP

FCT, Abuja - Kotun daukaka kara da ke zamanta a Abuja ta soke hukuncin da babbar kotun tarayya na ranar 7 ga watan Yuli, 2022 da ya kori kakakin majalisar Delta Sheriff Oborevwori a matsayin dan takarar gwamna a PDP a zabe mai zuwa.

Rahoton jaridar The Nation ya ce an aiwatar soke wannan hukunci na babbar kotu ne a yau Litinin 29 ga watan Agusta, 2022.

Kara karanta wannan

Ta tabbata: Dan a mutun Kwankwaso ya rasa kujerar shugabancin PDP a Kano

Wani kwamitin kotu karkashin jagorancin mai shari’a Peter Ige, ya bayyana cewa babbar kotun tarayya ba ta da hurumin sauraran karar da David Edevbie ya shiga.

An soke karar korar Oborewori a matsayin dan takarar gwamnan PDP a Delta
Kotun Daukaka Kara Ta Soke Korar Kwace Tikitin Oborevwori a Matsayin Dan Takarar Gwamnan Delta Na PDP | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Kwamitin mai mutane uku ya ci gaba da cewa, Edevbie ya gaza kawo hujjar cewa Oborevwori ya ba da takardun bogi na kammala karatun ga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) saboda samun damar tsayawa karar gwamna.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Alkali ya yi kurkure

Ya kara da cewa Mai shari’a Taiwo da yanke hukuncin a ranar 7 ga watan Yuli, 2022, ya tafka kuskure lokacin da ya amince da ikirarin Edevbie.

Sun ce, Taiwo, wanda a yanzu ya yi ritaya ya saba lamba ganin cewa abubuwan da ya duba ya yi hukuncin basu cancanta ba saboda har yanzu ba a ba INEC sunan Oborevwori ba.

Duba da wannan, mai shari’a Ige ya tabbatar da cin nasarar Oborevwori a zaben fidda gwanin PDP na ranar 25 ga watan Mayu.

Kara karanta wannan

Karfin hali: An kama wani sojan bogi da ke yiwa mata fashi da makami

Channels Tv ta ce, Oborevwori ya lashe zaben da kuri’u 590 inda ya doke Edevbie da ya samu kuri’u 113 kacal.

Shekarau ya yi alkawarin kawo kuri'un Kano da sauran jihohi ga Atiku a zaben 2023

A wani labarin kuma, bayan sake zama mamba a jam'iyyar PDP, Mallam Ibrahim Shekarau ya dauki alkawurra ga dan takarar shugaban na jam'iyyar PDP.

A yau Litinin 29 ga watan Agusta ne tsohon gwamnan jihar Kano, kuma sanatan Kano ta tsakiya, Ibrahim Shekarau ya sake shiga inuwar jam’iyyar adawa ta PDP bayan ya shafe 'yan watanni da 'yan kayan marmari a NNPP.

Shekarau ya shiga NNPP ne tare da 'yan a mutunsa bayansa a ranar 18 ga watan Mayu, biyo bayan dambarwar da ta barke tsakaninsa da gwamnan Kano na yanzu; Abdullahi Ganduje kan rikon shugabancin APC a jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel