Shekarau ya yi alkawarin kawo kuri'un Kano da sauran jihohi ga Atiku a zaben 2023

Shekarau ya yi alkawarin kawo kuri'un Kano da sauran jihohi ga Atiku a zaben 2023

  • Tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau ya bayyana ficewa daga jam'iyyar NNPP zuwa PDP
  • Shekarau ya yiwa dan takarar shugaban kasa na PDP alkawarin kawo kuri'un jihar Kano da sauran jihohi
  • Manyan jiga-jigan jam'iyyar PDP ne suka dira jihar Kano domin sake karbar Shekarau zuwa jam'iyyar PDP

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jihar Kano - Bayan sake zama mamba a jam'iyyar PDP, Mallam Ibrahim Shekarau ya dauki alkawurra ga dan takarar shugaban na jam'iyyar PDP.

A yau Litinin 29 ga watan Agusta ne tsohon gwamnan jihar Kano, kuma sanatan Kano ta tsakiya, Ibrahim Shekarau ya sake shiga inuwar jam’iyyar adawa ta PDP bayan ya shafe 'yan watanni da 'yan kayan marmari a NNPP.

Shekarau ya shiga NNPP ne tare da 'yan a mutunsa bayansa a ranar 18 ga watan Mayu, biyo bayan dambarwar da ta barke tsakaninsa da gwamnan Kano na yanzu; Abdullahi Ganduje kan rikon shugabancin APC a jihar.

Kara karanta wannan

Yadda Malam Shekarau ya Canza Jam’iyya Sau 4 a Shekaru 8 Daga 2014 Zuwa 2022

Alkawarin da Shekarau ya yiwa Atiku a Kano
Shekarau ya yi alkawarin kawo kuri'un Kano da sauran jihohi ga Atiku a zaben 2023 | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Da shekarau aka kirkiri jam'iyyar PDP a 2013, kuma ya kasance mamban jam’iyyar PDP lokacin da ya lashe zaben gwamna tsakanin shekarun 2003 zuwa 2011, Premium Times ta ruwaito.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Alkawarin Shekarau ga Atiku

Jim kadan bayan ayyana shiga PDP, Shekarau ya dauki wani alkawari a gaban dan takarar shugaban kasan PDP, Atiku Abubakar da dan takarar mataimakin shugaban gwamna Okowa.

Da yake jawabi ya ce:

"Ni, da ilahirin dubban mabiyana mun sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP, kuma a yanzu mun zama 'yan a mutun PDP.
“Na rubutawa kukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) wasika a hukumance cewa ni yanzu ba dan takarar Sanata ne a karkashin jam’iyyar NNPP ba.

Tsohon gwamnan ya ce zai yi kokarin ganin Atiku ya samu kuri'un Kanawa da sauran jihohin kasar nan.

Kara karanta wannan

Bayan Karban Tuban Shekarau, Atiku Ya ba da Tallafin Miliyoyi Ga Waɗan Da Ambaliya Ta Shafa a Kano

Wadanda suka halarci taron

Baya ga Atiku da abokin takararsa Okowa, wasu jiga-jigan PDP sun halarci taron da ya samu halartar dubban jama'a a jihar Kano, Daily Trust ta ruwaito.

Sauran jiga-jigan PDP a taron sun hada da gwamnonin Sokoto da Taraba, Aminu Waziri Tambuwal da Darius Ishaku.

Sauran kuwa sun hada da tsohon mataimakin shugaban kasa, Namadi Sambo, shugaban BOT na PDP, tsoffin gwamnonin Jigawa; Saminu Turaki da Sule Lamido, tsohon gwamnan Sokoto, Attahiru Bafarawa, na Kaduna, Ahmed Makarfi, na Adamawa Boni Haruna da dai sauransu.

Kwankwaso Mayaudari Ne, Ya Yaudaremu, Inji Tsohon Gwamnan Kano Shekarau

A wani labarin, Malam Ibrahim Shekarau, ya bayyana yadda Sanata Rabiu Kwankwaso, ya yaudare shi da ma magoya bayansa bayan da ya jawo su zuwa jam'iyya mai kayan marmari ta NNPP a watan Mayu.

Shekarau da Kwankwaso dukkansu tsoffin gwamnoni ne a Kano, jiha mafi tashen kasuwanci a Arewa maso Yammacin Najeriya, Leadership ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Shekarau Ya Sauya Sheka Zuwa PDP, Bayan Wata 3 Rak a NNPP

A yau Litinin, 22 ga watan Agusta, Shekarau ya shaida wa manema labarai cewa, zai bayyana matsayinsa na yiwuwar sauya sheka da NNPP zuwa wata jam'iyyar nan ba da jimawa ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel