Ana Tsakiyar Rikici a PDP, Atiku Zai Kafa Kwamitin Da Za Su Yi Masa Yakin Zabe

Ana Tsakiyar Rikici a PDP, Atiku Zai Kafa Kwamitin Da Za Su Yi Masa Yakin Zabe

  • Alhaji Atiku Abubakar da jam’iyyar hamayya ta PDP sun kammala shirin kafa kwamitin yakin neman kujerar shugabancin kasa a zabe mai zuwa
  • Ana tunani rigimar da ta kunno kai a jam’iyyar ne ta hana tun tuni an san wadanda za su taya Atiku Abubakar yakin zama shugaban Najeriya
  • Bisa dukkan alamu PDP ta gaji da jiran a sasanta da Nyesom Wike, za ta kaddamar da kwamitocin neman takara ko ba a gama yin sulhu ba

Abuja - Alamu na nuna cewa a ranar Litinin 22 ga watan Agusta 2022, Atiku Abubakar da jam’iyyar PDP sun kammala aikin kwamitin yakin zabe.

Daily Trust ta kawo rahoto a ranar Talatar nan cewa jam’iyyar hamayya ta PDP da ‘dan takaranta sun gama zakulo wadanda su taya ta yin kamfe a 2023.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Wike Ya Sha Alwashin Ganin-Bayan ‘Yan PDP a Ribas da ke tare da Atiku

Alhaji Atiku Abubakar ya kai ga daukar wannan mataki ne a yayin da jam’iyyar adawar ta ke tsundume cikin rikicin gida da bangaren Nyesom Wike.

Shugabannin jam’iyyar sun yi ta kokarin ganin an dinke barakar, amma abin ya gagara. Wannan ya hana majalisar koli ta NEC tayi zama tuni a Abuja.

Wata majiya ta shaidawa jaridar cewa ganin rikicin ya ki cinyewa, wasu jagororin jam’iyya sun ba ‘dan takaran shawara ya rantsar da kwamitin kamfe.

An kai matakin da dole PDP za ta fara shiryawa zaben 2023 ba tare da jiran wani ‘dan jam’iyya ba. Irin wannan labari ya zo a jaridar nan ta Vanguard a jiya.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Atiku Abubakar
Atiku Abubakar a taron NBA Hoto: @Atikuorg
Asali: Facebook

Dole ayi gaba, a kafa kwamiti

“Mun yaba da Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike a matsayin babban jigo a jam’iyyar nan, ya da matukar amfani a gare mu.

Kara karanta wannan

Atiku: Sai na mai da jami'o'in tarayya karkashin gwamnatin jiha idan na gaji Buhari a 2023

Amma sauran ‘ya ‘yan jam’iyya ma su na da amfani. Dole mu yi gaba.”

Zuwa yanzu Legit.ng Hausa ba ta da masaniya a kan wadanda Atiku Abubakar zai dauka a kwamitin.

Kakakin Atiku ya yi magana

Da aka tuntubi mai magana da yawun bakin ‘dan takaran shugabancin kasar, Paul Ibe a game da wannan batu, sai ya nuna cewa za a tafi da kowa a neman zabe.

A cewar Paul Ibe, Atiku Abubakar zai yi amfani da duk wani babba a jam’iyyar PDP wajen ganin ya lashe zaben shugaban kasa da za ayi a farkon shekarar 2023.

Ayi sulhu da Wike - Jang

An ji labari Sanata Jonah Jang ya kaddamar da ayyukan Nyesom Wike a Ribas, inda ya bada shawara ta musamman ga ‘dan takararsu na shugaban kasa a PDP.

Tsohon Gwamnan Filato ya fadawa Atiku Abubakar cewa sai ya dinke barakar da ke PDP ta hanyar yin sulhu da kowa, sannan zai iya zama Shugaban kasa a 2023.

Kara karanta wannan

2023: Tsohon Gwamna Ya Fadawa Atiku Abin da Zai Yi Idan Yana Son Cin Zabe

Asali: Legit.ng

Online view pixel