Rikicin PDP: Wike Ya Sha Alwashin Ganin-Bayan ‘Yan PDP a Ribas da ke tare da Atiku

Rikicin PDP: Wike Ya Sha Alwashin Ganin-Bayan ‘Yan PDP a Ribas da ke tare da Atiku

  • Gwamna Nyesom Wike ya aika sako a kaikaice ga ‘ya ‘yan jam’iyyar PDP a jihar Ribas da ke aiki ta bayan fage da Atiku Abubakar
  • Bisa dukkan alamu Gwamnan na Ribas yana yakar wadanda ba su goyon bayansa a rigimar cikin gidan da ya dabaibaye jam’iyyar PDP
  • Mai girma Gwamnan ya ja-kunnen mutanen jiharsa da cewa babu wani wanda zai bar bangarensa, ya koma goyon bayan ‘yan adawansa

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Rivers - Wasu jagororin jam’iyyar PDP a Ribas da suke goyon bayan Alhaji Atiku Abubakar a kan Nyesom Wike sun samu kansu a cikin halin ha’ula’i.

Jaridar Vanguard ta kawo rahoto cewa dole wadanda suke adawa da Mai girma Gwamna Nyesom Wike a jam’iyyar PDP su tattara su fice daga Ribas.

Hakan na zuwa ne bayan Gwamnatin Wike ta fara farautar ‘yan adawanta, wadanda suke marawa Atiku Abubakar baya a zaben shugaban kasa a 2023.

Kara karanta wannan

2023: Tsohon Gwamna Ya Fadawa Atiku Abin da Zai Yi Idan Yana Son Cin Zabe

Gwamna Wike ya shaidawa ‘ya‘yan jam’iyyar hamayya ta PDP cewa babu wanda ya ci moriyar gwamnatinsa da yanzu zai hada-kai da masu adawa da shi.

An rahoto Wike yana cewa duk wanda ya nemi ya marawa abokan adawarsa baya, bai isa ya tserewa fushinsa ba, da alama dai yana nuni ne ga Atiku.

“Duk mai neman fada da mu, za mu yaki wannan mutumi. Da zarar yau ka na tare da mu, gobe ka koma wajen abokin gabanmu, za mu yi amfani da duk karfin da mu ke da shi, sai ma mun fara kammalawa da makiyanmu, sannan za mu gama da kai.”

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Gwamna Nyesom Wike
Nyesom Wike ya gayyato Gwamnan Legas
Asali: Twitter

Gargadi ga masu tada zaune tsaye

Daily Post tace Gwamnan na Ribas ya kuma gargadi duk wani ‘dan siyasa a kowace jam’iyya a kan neman kawowa jiharsa barazana ta fuskar tsaro.

Kara karanta wannan

‘Yan Sanda Sun Cafke Wanda Ake Zargi Yana Neman Kashe Tsohon Shugaban Majalisa

“Kowa ya bude kunnensa, ko kana jam’iyyar PDP, APC, ko kana SDP ne ko Accord ko wata jam’iyya, idan na kama ka, za kayi bayani ne.
Ba zan bari wani ya tada zaune tsaye a jihar nan ba. Mun yi fama da rashin tsaro kuma Ubangiji ya taimake mu a sanadiyyar jami’an tsaro.
A waje na, ko gaskiya ne, ko da ba gaskiya ba ne, dole in tabbatar mun dauki mataki."

Su wanene ke rigima da Wike?

Majiyar tace wadanda ake zargi su na tare da Atiku a PDP na Ribas sun hada da Austin Opara, Sanata Lee Maeba da tsohon Gwamna Celestine Omehia.

Haka zalika akwai jiga-jigan jam’iyya irinsu Jones Ogbonda, Ikechi Chinda, da Chinyere Igwe.

Atiku ya nemi sulhu - Jang

An samu labari Jonah Jang ya kaddamar da ayyukan Nyesom Wike a Ribas, ya bada shawara ta musamman ga ‘dan takarar shugabancin Najeriya a PDP.

Tsohon Gwamnan na Filato ya fadawa Atiku Abubakar cewa sai ya dinke barakar da ke PDP ta hanyar yin sulhu da Wike, sannan zai iya lashe zabe a 2023.

Kara karanta wannan

Jigon APC ya Jero Abubuwan da za su Hana Atiku Abubakar Samun Nasara a 2023

Asali: Legit.ng

Online view pixel