Taron NBA: Abin da Atiku, Obi suka fada, yayin da aka nemi Kwankwaso aka rasa

Taron NBA: Abin da Atiku, Obi suka fada, yayin da aka nemi Kwankwaso aka rasa

  • Rabiu Musa Kwankwaso bai je taron kungiyar NBA na shekarar nan ba, duk da an gayyaci ‘dan takaran shugaban kasar na NNPP
  • Atiku Abubakar, Peter Obi, da Kashim Shettima sun yi baja-kolin manufofin da za su aiwatar idan har suka yi sa’ar samun mulki
  • Sanata Kashim Shettima ya wakilci Tinubu, amma Kwankwaso bai iya aiko ko da wakili zuwa wannan gagarumin taron Lauyoyi ba

Lagos – Legit.ng Hausa ta fahimci a ranar Litinin, 22 ga watan Agusta 2022, aka soma taron kungiyar Lauyoyi watau NBA na shekarar nan a garin Legas.

Kungiyar NBA ta aika goron gayyata ga manyan ‘yan takaran shugaban Najeriya hudu; Atiku Abubakar, Bola Tinubu, Peter Obi da Rabiu Kwankwaso.

Vanguard tace Atiku Abubakar da Peter Obi sun halarci taron yayin da Bola Tinubu ya aiko da abokin takararsa, Kashim Shettima domin ya wakilce shi.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Ɗumi: Tinubu Ya Yi Watsi da Kwankwaso, Ya Fadi Manyan Yan Takara Uku da Zasu Fafata a 2023

Da ya tashi jawabi, an rahoto Atiku Abubakar yana cewa zai damka jami’o’i ga gwamnatocin jihohi idan ya zama shugaban kasa, domin samun kula.

Ganin halin yajin-aiki da karancin kudi da ake fama da shi, ‘dan takaran na PDP yace gwamnatin tarayya ba za ta iya daukar dawainiyar karatun jami’a ba.

Rahotonni sun ce Atiku ya koka a kan yadda al’umma ke rayuwa cikin talauci da rashin aiki yi. A gefe, an ji Peter Obi ya yi tarayya da shi a kan wannan.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Taron NBA
Hotunan taron NBA Hoto: Hotunan taron NBA Hoto: @novieverest, @Rasheethe, @General_Oluchi
Asali: Twitter

‘Dan takaran LP yace yadda za a shawo kan tattalin arzikin Najeriya shi ne a rika hada abubuwan da ake bukata a gida, a daina dogaro da kasashen ketare.

Premium Times ta rahoto Obi yana cewa sai Najeriya ta na fitar da kaya zuwa waje, tana samun Daloli sannan darajar Naira da ya karye zai dawo daidai.

Kara karanta wannan

2023: Tinubu ya fadi babban sauyin da zai kawo a aikin 'yan sanda idan ya gaji Buhari

Shi kuwa Kashim Shettima wanda ya wakilci Bola Tinubu a wajen yace hanyar bunkasa tattali shi ne gwamnati ta fadada hanyoyin samun kudin shigarta.

The Cable tace Sanata Shettima ya bada misalin yadda ya gina makarantun kwarai a lokacin yana gwamna a Borno, ya kuma tallata takarar Tinubu a taron.

Ina Kwankwaso ya shiga?

Mun fahimci Rabiu Kwankwaso mai neman shugabancin Najeriya a NNPP, bai je wannan gagarumin taro ba duk Olumide Akpata ya aika masa takarda.

Tsohon gwamnan na Kano ya bada uzurin cewa ayyuka sun yawa a wannan lokaci, sannan kuma abokin takararsa bai kasar don haka ya gagara turo wakili.

Ana wannan sai aka ji Kwankwaso ya gana da irinsu Amb. Sukubo Sara-Igbe Sukubo da wasu 'ya 'yan jam'iyyarsu ta NNPP daga jihar Taraba a gidansa a Abuja.

Peter Obi ya dace da mulki

A yau mu ka rahoto Ayo Adebanjo wanda shi ne shugaban ‘Yan Afenifere ya bayyana abin da ya sa Southern and Middle Belt Leaders’ Forum ke tare da LP.

Kara karanta wannan

Wasu Shugabannin PDP na Neman Tada Rikici, Sun ce An Ware Su a Yakin Zaben Atiku

Kungiyar Afenifere mai kare hakkin Yarbawa tace Bola Tinubu da Atiku Abubakar ba su dace da mulki ba domin yanzu Ibo ya kamata su karbi shugabanci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng