2023: Tikitin Musulmi Da Kirista Da Muka Yi A Baya Bai Tsinana Mana Komai Ba, Oshiomhole

2023: Tikitin Musulmi Da Kirista Da Muka Yi A Baya Bai Tsinana Mana Komai Ba, Oshiomhole

  • Adams Oshiomhole, tsohon shugaban jam'iyyar APC na kasa ya yi tsokaci kan batun tikitin musulmi da musulmi na shugaban kasa a jam'iyyar
  • Oshiohole ya ce yana goyon bayan tikitin musulmi da musulmin domin yan takarar sun cancanta kuma ko da ake zaben musulmi da kiristan ba su tsinana wa kasar komai ba a baya
  • Tsohon gwamnan na Jihar Edo ya yi watsi da batun cewa Tinubu zai musuluntar da Najeriya yana mai cewa bai iya musuluntar da iyalansa ba balantana kasa tunda matarsa ma fasto ce

Tsohon Gwamna Jihar Edo kuma tsohon shuganban APC na kasa, Adams Oshiomhole ya yi watsi da koken da wasu ke yi kan zaben musulmi a matsayin abokin takara da Ahmed Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasar jam'iyyar ya yi.

Kara karanta wannan

Musulmi da Musulmi: Kada ku yarda wani fasto ko limami ya fada maku wanda za ku zaba, Keyamo ga yan Najeriya

Oshiomhole ya ce lokaci ya yi a kasar da za a yi watsi da son zuciya da kuma abin da zuciya ke ji irin addini da kabilanci a mayar da hankali kan cancanta domin ceto kasar.

Adams Oshiomhole.
2023: Tikitin Musulmi Da Kirista Da Muka Yi A Baya Bai Tsinana Mana Komai Ba, Oshiomhole. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Da ya ke magana a TVC a ranar Alhamis, tsohon gwamnan ya bayyana gamsuwarsa da tikitin musulmi da musulmi a APC, ya kuma jinjinawa Tinubu kan zabin, rahoton Daily Trust.

Tinubu ya dauki Kashim Shettima, tsohon gwamnan Jihar Borno a matsayin mataimakinsa.

"Muna bukatar karfin hali. Munyi sha wahala wurin kokarin daidaita kan wannan batun addinin a shekarun baya. Zabin Tinubu ya nuna zai iya daukan matakai masu wahala idan an zabe shi.
"Idan adadin masallatai da coci da muka gina tsawon shekarun nan sunyi daidai da masana'antu, ba za mu kasance irin talaucin da muke ciki ba."

Kara karanta wannan

2023: Tinubu ya ci zabe ya gama, In ji tsohon dan takarar kujerar gwamna a Plateau

Oshiomhole ya kara da cewa ya gamsu da zabin Shettima saboda cancantarsa da wasu nasarorin da ya samu.

Ya ce:

"Ba za mu cigaba da harka kamar yadda aka saba a baya ba. Na gamsu da cancantar Shettima. Yana da ilimi da wayewa. An karrama shi a gida da waje.
"Mu yi amfani da lokaci wurin duba hali da cancantar wanda Tinubu ya zaba. Nan bada dadewa ba, marasa addini za su fito su ce ba haka ba."

Oshiomhole ya yi watsi da zargin cewa Tinubu zai musuluntar da Najeriya

Tsohon shugaban na APC ya yi watsi da zargin cewa Tinubu zai musuluntar da kasar yana mai cewa ya ma kasa musuluntar da iyalansa duba da cewa matarsa kirista ce kuma fasto.

Tikitin Musulmi Da Musulmi Kaddara Ce Daga Allah, Shugaban APC, Adamu

A bangarensa, Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Abdullahi Adamu, a ranar Laraba, ya bawa kiristoci tabbacin cewa babu abin tsoro game da tikitin musulmi da musulmi na Sanata Kashim Shettima da Asiwaju Tinubu a zaben shugaban kasa na 2023.

Kara karanta wannan

Tikitin Musulmi Da Musulmi Kaddara Ce Daga Allah, Shugaban APC, Adamu

Ya ce zabin musulmi da musulmi na jam'iyyar a zaben shugaban kasar "kaddara ce ta Allah."

Adamu ya yi wannan jawabin ne a Daura lokacin da ya jagoranci Kwamitin Ayyuka na Jam'iyyar yayin ziyarar Sallah da suka kaiwa Shugaba Muhammadu Buhari, rahoton The Punch.

Asali: Legit.ng

Online view pixel